Zamu Duba Yiwuwar Kafa Dokar Hana Makiyaya Kiwon Fili a Jihar Shugaban Kasa, Gwamna

Zamu Duba Yiwuwar Kafa Dokar Hana Makiyaya Kiwon Fili a Jihar Shugaban Kasa, Gwamna

  • Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, yace gwamnatinsa zata diba yiwuwar hana kiwon fili a faɗin jihar
  • Masari ya bayyana cewa kafin kafa dokar gwamnati zata samar da filin kiwo ga makiyaya
  • A cewarsa, Gwamnatin tarayya ta turawa Katsina biliyna N6.2bn, kuma a matakin jiha za'a zuba wasu kuɗaɗen

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace gwamnatinsa zata duba yuwuwar hana makiyaya kiwon fili a faɗin jihar.

Masari ya yi wannan jawabi ne a cikin shirin 'Politics Today' na kafar watsa labarai ta Channels tv ranar Litinin.

Gwamnan ya yi watsi da yadda makiyayan suke yawo daga wannan yankin zuwa wani a faɗin ƙasa.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari
Zamu Duba Yiwuwar Kafa Dokar Hana Makiyaya Kiwon Fili a Jihar Shugaban Kasa, Gwamna Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Sai dai ya bayyana cewa kafin gwamnatinsa ta hana makiyaya kiwon dabbobinsu a fili, sai ta tabbatar ta samar musu wurin da zai zame musu gida, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allah zai bamu shugaba kamar Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

Shin kiwon fili ya saba wa musulunci?

A jawabinsa, Masari yace:

"Muna kokarin hana makiyaya yawo da shanu a fili, amma kafin mu kafa dokar zamu tabbatar mun samar musu da wurin kiwo."
"Kamata ya yi makiyaya su zauna a wuri ɗaya, yawo da dabbobi ko ina ba abu bane mai kyau, ina tunanin ya sabawa addinin musulunci."
"Me zai sa ka mallaki dabbobin da ba zaka iya ciyar da su ba? kuma ka dinga zuwa gonakin mutane kana musu ɓanna kuma kace shin hakan dai-dai ne? Bana tunanin haka abu ne mai kyau."

Wane mataki Masari zai ɗauka?

Bugu da kari Masari yace a kokarin da suke na fara shirin zamantar da kiwon dabbobi, gwamnatin tarayya ta turo biliyan N6.2bn.

Gwamnan yace:

"Mun dade da fara aiwatar da shirin, FG ta bamu biliyan N6.2bn kuma munanan a matakin jiha zamu zuba biliyan N6.2bn. Manufar mu itace mu samar wa fulani wuri ɗaya da zasu zauna."

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun kashe mace mai juna biyu a Zaria

Babu shirin katse sabis na sadarwa a Katsina

A wani labarin kuma Bayan Datse Sabis a Zamfara, Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Datse Sabis a Jihar Katsina

Gwamnatin tarayya ta musanta jita-jitar cewa ta bada umarnin a katse sabis din layukan sadarwa a jihar Katsina.

Shugaban hukumar sadarwa ta ƙasa NCC, Farfesa Danbatta, yace labarin ba shi da tushe ballantana makama, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel