Tashin hankali yayin da sojojin Guinea suka kame shugaban kasa, suka kwace mulki
- Rahoto daga kasar Guinea ya bayyana cewa, wasu sojojin sun kitsa juyin mulki kuma sun kwace kasa
- Sai dai, a bangare guda, fadar shugaban kasar ta ce hakan bata faru ba a cikin wani bidiyo da ta fitar
- A halin yanzu kasar na cikin dardar yayin da ake kokarin gano halin da gwamnatin kasar ke ciki
Guinea - Rahoton BBC ya nuna cewa ba a san makomar shugaban kasar Guinea, Alpha Condé ba bayan wani faifan bidiyo da ba a tantance ba ya nuna shugaban a hannun sojoji, wadanda suka ce sun yi juyin mulki a kasar.
Legit.ng ta tattaro cewa, ministan tsaron kasar, duk da haka, an ambato shi yana cewa yunkurin juyin mulkin ya ci tura.
A cewar rahoton, wannan ya biyo bayan harb -harben da aka shafe sa'o'i ana yi a kusa da fadar shugaban kasa a Conakry babban birnin kasar yayin da sojoji ke sintiri kan titunan da ba kowa a kai.
Rahoton ya nuna cewa firgitattun mazauna gundumar Kaloum ta tsakiya sun bi umarnin su na zama a gida.
Bidiyon ya nuna sojoji daga wata runduna ta musamman inda suke tambayan Shugaba Condé da ya tabbatar da cewa bai ji rauni ba amma ya ki amsawa, ya kara da cewa an rufe dukkan iyakokin kasa da na sama sannan gwamnati ta wargaza.
Sojoji sun kwace mulki a Guinea
A wani rahoto da gidan talabijin na Channels ya fitar, ya bayyana cewa, sojoji a kasar tuni suka kwace mulkin, inda suka tsare shugaban kasar.
Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba
Wani jami'i sanye da kayan sojoji da ke cikin bidiyon da aka aika wa AFP, ya bayyana cewa:
"Mun yanke shawarar, bayan mun dauki shugaban kasa, za mu rusa kundin tsarin mulki."
Jami'in ya kuma ce an rufe iyakokin kasa da na sama na Guinea kuma gwamnati ta rushe.
Sai dai, a bangare guda ba a san halin da ake ciki ba yayin da gwamnatin Conde ta fitar da wata sanarwar da ta saba batun jami'in sojan da ke cewa an dakile harin da aka kaiwa fadar shugaban kasa.
Boko Haram: Amurka ta fadi dalilin da yasa Najeriya ba za ta zama kamar Afghanistan ba
A wani labarin, Kasar Amurka ta ba Najeriya tabbacin cewa maimaita abin da ya faru a Afganistan ba zai taba faru ba a Najeriya dake Afrika ta yamma, The Punch ta ruwaito.
Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard ce ta bayar da wannan tabbacin ranar Litinin 30 ga watan Agusta yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Jakadiyar ta yi bayanin cewa yanayin Najeriya da Afghanistan ba daya bane.
Asali: Legit.ng