Bayan Ganawa da Shugaba Buhari, Sanatan Ndume Ya Sake Magana Kan Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya

Bayan Ganawa da Shugaba Buhari, Sanatan Ndume Ya Sake Magana Kan Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya

  • Sanata Ali Ndume, na jam'iyyar APC, yace har yanzun yana kan maganarsa ta farko cewa a gurfanar da tubabbun yan Boko Haram
  • Sanatan ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja jim kaɗan bayan ganawa da Buhari
  • Ndume, wanda shine shugaban kwamitin rundunar sojin ƙasa, yace ya kamata sojoji su binciki masu mika wuya

Abuja - Sanata Ali Ndume, sanata mai wakiltar Borno ta kudu, yace mayakan Boko Haram da suka mika wuya, "Waɗanda akwai sauran burbushin ta'addanci a zukatansu, kamata yayi a binciko su, a hukunta su."

Da yake jawabi a Abuja, jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, sanatan ya jaddada cewa bai kamata a saki jiki da tubabbun lokaci guda ba, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Sanatan yace ya kamata gwamnati ta bi dokar ƙasa da kuma ta kasa-da-kasa wajen amsar tubabbun yan ta'addan.

Sanata Ali Ndume
Bayan Ganawa da Shugaba Buhari, Sanatan Ndume Ya Sake Magana Kan Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ina nan kan baka ta - Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume yace:

"Har yanzun ina nan akan magana ta kan yan ta'addan dake mika wuya, wasu ne kawai suke fassara zance na ta yadda ransu yake so."
"Akwai dokar ƙasa da ta yi bayani kan irin haka, hakazalika akwai dokokin kasa-da-kasa da suka yi bayani kan irin haka saboda wannan ba shine karo na farko da aka samu irin wannan ƙalubalen a kasashen duniya ba."
"Duk lokacin da ka fita fagen yaki, kodai ka ci nasara ko abokin faɗanka ya mika wuya, idan ya mika wuya ka rasa damar hukunta shi amma ba zaka ce ba shi da laifi ba."

Ya kamata a bi dokar kasa-da-kasa

Ndume ya kara jaddada cewa yana nan kan bakarsa game da tubabbun yan Boko Haram, amma ya kamata abi tsarin dokar kasa da kuma ta kasashen duniya.

Punch ta ruwaito Sanatan yace:

"A amince musu, a ɗauki bayanansu, sannan a bincike su, waɗanda suka mika wuya dagaske a kyale su, amma duk wandanda akwai ɓurɓushin tunanin ta'addanci a zuciyarsu, a gurfanar da su."
"Idan mutum ya mika wuya a ba shi dama, matukar ka tuba to baza'a hukunta ka kai tsaye ba, za'a baka dama kaje kotu ka tabbatar da tubarka ko akasin haka, wannan shi nake bukata gwamnati ta yi."

A wani labarin kuma Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, Gwamna El-Rufa'i Ya Bayyana Rashin Jin Dadinsa

Hukumar zaben jihar Kaduna (KADSIECOM) tace an lalata tare da sace wasu na'urorin da aka tanaza don zaben kananan hukumomi.

Shugabar Hukumar, Saratu Dikko, tace an kaiwa ma'aikata hari a kananan hukumomin Giwa da Igabi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel