Jam'iyyar PDP Ta Lallasa El-Rufa'i da APC a Zaɓen Kansila Na Gundumar Gwamnan Kaduna

Jam'iyyar PDP Ta Lallasa El-Rufa'i da APC a Zaɓen Kansila Na Gundumar Gwamnan Kaduna

  • Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a zaɓen kansila na gundunar gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i
  • Baturen zaɓen gundumar ta Unguwan Sarki, Mohemmed Usman, yace ɗan takarar PDP ya lashe zaɓen kansila a yankin
  • Gwamna El-Rufa'i yace jam'iyyar APC ba zata yi magudi ba kuma ba ta tsammanin sauran jam'iyyu zasu yi maguɗi a zaɓen

Kaduna - Ɗan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zaɓen kansila da aka gudanar a Unguwan Sarki, gundumar gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, baturen zaɓen gundumar, Mohammed Usman, yace ɗan takarar PDP, Abdulhalim Na’ibi, ya samu kuri'u 1,405.

Yayin da ya kada abokin takararsa na jam'iyyar APC mai mulki, Aliyu Farouk, wanda ya samu kuri'u 804.

Malam Nasiru da Zababben Kansilan Unguwan Sarki
Jam'iyyar PDP Ta Lallasa El-Rufa'i da APC a Zaɓen Kansila Na Gundumar Gwamnan Kaduna Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Baturen zaɓen yace:

Kara karanta wannan

Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa'i Ya Magantu

"Saboda haka Abdulhalim Usman Na’ibi, na jam'iyyar PDP shine zaɓaɓɓen kansila a Unguwan Sarki, bayan cika ka'idoji da dokoki kuma ya samu kuri'u masu rinjaye."

Mutane su fito su zaɓi wanda suke so - El-Rufa'i

Kafin ranar zaɓen, Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i, ya shaidawa manema labarai cewa za'ai amfani da na'urar EVM wajen zaɓen domin tabbatar da an yi wa kowa adalci kuma an yi amfani da kuri'un jama'a.

Gwamnan yace:

"Kamar yadda nake faɗa a lokuta da dama, ba zamu zalinci jama'a kamar yadda wasu jam'iyyu ke yi ba, zamu tabbatar an kidaya kuri'un mutane."
"Ba dole bane sai APC ta lashe kowane zaɓe amma kuma bamu son wasu jam'iyyu su mana maguɗi. Saboda hakane muka karafafawa hukumar zaɓe guiwa ta samar da yanayin zaɓe mai tsafta."

A wani labarin kuma Bayan Ganawa da Shugaba Buhari, Sanatan Ndume Ya Sake Magana Kan Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnati Tare da Wasu Mutum 50,000 Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

Sanata Ali Ndume, na jam'iyyar APC, yace har yanzun yana kan maganarsa ta farko cewa a gurfanar da tubabbun yan Boko Haram

Sanatan ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja jim kaɗan bayan ganawa da Buhari.

Ndume, wanda shine shugaban kwamitin rundunar sojin ƙasa, yace ya kamata sojoji su binciki masu mika wuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel