Zaben kananan hukumomin Kaduna: PDP ta lallasa APC a akwatin mazabar Gwamna El-Rufa'i
- Gwamna El-Rufa'i ya rasa akwatin zabensa ga jam'iyyar PDP a zaben kananan hukumomi
- Gwamnan ya kada kuri'arsa da safiyar Asabar a akwatin zaben
- A cewar El-Rufa'i, ba dole bane jam'iyyarsa ta lashe kowani zabe ba
Kaduna - Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ta lashe akwatin zabe kujerar shugaban karamar hukumar da kuma na kansila a mazabar gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i.
El-Rufa'i ya kada kuri'arsa da safe a akwatin mazabarsa dake Unguwar Sarki, karamar hukumar Kaduna ta Arewa, rahoton ChannelsTV.
Yayinda yake kada kuri'arsa, El-Rufa'i ya bayyana cewa bai zama dole jam'iyyarsa ta APC ta kashe zabe ba, kawai abinda yake bukata shine inganta zabe ta hanyar amfani da na'urar zamani.
A cewar gwamnan, kawo wannan na'urar ua nuna cewa gwamnatin APC a jihar Kaduna ba tada shirin magudin zabe.
Yayin sanar da sakamakon zaben, baturen zaben mazabar, Muhammad Sani, ya ce jam'iyyar APC ta samu kuri'u 62 a zaben shugaban karamar hukumar, yayinda PDP ta samu kuri'u 86.
A zaben Kansila kuwa, APC ta samu kuri'u 53 yayinda PDP ta samu kuri'u 100.
Yanzu haka, ana cigaba da tattara sakamakon zabe a matattarar zabe na karamar hukumar Kaduna ta kudu.
An Ɗage Zaɓukan Ƙananan Hukumomi 4 a Jihar Kaduna
Mun kawo muku cewa hukumar zabe mai zaman kanta na Jihar Kaduna, KADSIECOM, ta dage zabukan kananan hukumomi da aka shirya yi a ranar Asabar a kananan hukumomi hudu a jihar saboda rashin tsaro.
Hukumar, a ranar Juma'a, ta ce an dage zabukan ne biyo bayan samun rahoton tsaro wadda ya nuna ba zai yi wu a gudanar da zabukan ba cikin lumana a kananan hukumomin Kajuru, Birnin Gwari, Chikun da Zangon Kataf.
Rahoton na Daily Trust ya ce Shugaban hukumar, Dr Saratu Binta Dikko-Audu ya ce dagewar ya zama dole ne domin kare rayyuka da dukiyoyin mutane harda ma'aikatan zaben da kayan aiki.
Asali: Legit.ng