Ba boye-boye: Mu ‘yan siyasa ne muka jefa kasar a cikin matsala – Rochas Okorocha

Ba boye-boye: Mu ‘yan siyasa ne muka jefa kasar a cikin matsala – Rochas Okorocha

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya zargi 'yan siyasar Najeriya da sanya kasar a cikin matsalar da take fuskanta a yanzu
  • Jigon na APC ya ce idan da ace za a mika mulki ga masu kishin kasa, toh lallai da za a samu sauyi da kiraye-kirayen da wasu ke yi na a raba kasar
  • Ya kuma bayyana cewa mafita daya ga wannan hali da ake ciki shine a wayar da kan 'yan kasa, ta yadda za su fahimci irin makircin da ake shiryawa

Najeriya - Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar imo, ya yi zargin cewa ‘yan siyasar kasar nan na da hannu dumu-dumu a cikin tabarbarewar lamura da rashin hadin kai a tsakanin al’umman kasar.

Okorocha ya bayyana cewa rashin bawa ‘yan kasa masu kishinta damar mulkar kasar na daya daga cikin abubuwan da suka sanya ake samun karuwar masu son a raba kasar.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Ba boye-boye: Mu ‘yan siyasa ne muka jefa kasar a cikin matsala – Rochas Okorocha
Rochas Okorocha ya zargi yan siyasa da jefa kasar a halin da take ciki Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, tsohon gwamnan ya kara da cewa idan har masu rike da madafun iko suka amince da za su samar da hadin kai a tsakanin al’umma, shakka babu za a cimma manufa.

Sai dai kuma ya bayyana hakan a matsayin abu mai wahala saboda mafi akasarinsu kansu kadai suka sani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Mu muka janyo matsalolin da ake ciki a kasar nan ba kowa ba, a yanzu 'yan siyasa na yi ne domin cimma bukatun kansu, yawancin wadanda ke neman shugabanci dama suke nema su yi abun da suke nema a kan mulki."

Har ila yau ya kuma zargi 'yan siyasa da nuna bangaranci da kuma siyasar kabilanci, sannan ga lamarin rikicin addini da ake amfani da ita wajen kara raba kan al'umma.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Mafita ga halin da ake ciki

Ya kuma ce hanya daya da za a iya bi don magance wannan matsala ita ce wayar da kan 'yan kasa, ta yadda za su fahimci irin makircin da ake shiryawa da kuma manufar yin hakan.

Ya kara da cewa:

''Matsalar ita ce ba su gane ba ne, idan aka ganar da su za su fahimci cewa irin wadannan matsaloli ne suka hana Najeriya ci gaba, su suka haifar da rashin aikin yi da talauci da kuma siyasar kisa da cutar da jama'a."

Ya kuma yi nuni ga bukatar ganin an janyo matasa a jiki, ta yadda za a ba su dama su nuna bajintarsu a bangarorin shugabanci, ta yadda ba za su bayar da kunya ba duk lokacin da aka sakar musu ragama.

Arewacin Najeriya ta fi kowa shan azabar gazawar Buhari, Kungiyar Dattawan Arewa

A wani labari, kakakin kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Hakeem Baba-Ahmad, ya bayyana cewa Arewa ce tafi shan wahala sakamakon gazawar gwamnatin shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

Baba-Ahmad ya kara da cewa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da Peoples Democratic Party, PDP sun nuna cewa ba zasu iya magance matsalolin Najeriya ba.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a taron tattaunawa kan samar da hadin kai a Najeriya da kamfanin jaridar Ripples Najeriya ta shirya a Legas, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng