Arewacin Najeriya ta fi kowa shan azabar gazawar Buhari, Kungiyar Dattawan Arewa

Arewacin Najeriya ta fi kowa shan azabar gazawar Buhari, Kungiyar Dattawan Arewa

  • Dr Hakeem Baba-Ahmad ya ce yan Arewa sun fi kowa shan wahala a mulkin Buhari
  • Ya ce yan kudu su daina ganin laifin yan Arewa kan abubuwan da ke faruwa
  • Kamfanin Ripples Najeriya ta shirya taron tattauna matsalar rashin hadin kai a Najeriya

Lagos - Kakakin kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Hakeem Baba-Ahmad, ya bayyana cewa Arewa ce tafi shan wahala sakamakon gazawar gwamnatin shugaba Buhari.

Baba-Ahmad ya kara da cewa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da Peoples Democratic Party, PDP sun nuna cewa ba zasu iya magance matsalolin Najeriya ba.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a taron tattaunawa kan samar da hadin kai a Najeriya da kamfanin jaridar Ripples Najeriya ta shirya a Legas, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2023: APC na fuskantar sabuwar barazana yayin da Atiku da Obaseki suka hadu kan yadda PDP za ta kada jam'iyyar

Wasu manyan da suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa; shugaban kungiyar Afenifere, Pa Ayo Adebanjo da tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

Baba Ahmed yace:

"Arewacin Najeriya ce tafi shan azaba sakamakon gazawar shugaba Muhammadu Buhari."
"Ku daina daurawa Arewa laifin gazawar Buhari. Mutanen Arewa kawai sun yi rashin sa'ar daurashi a mulki ne kuma sune na gaba wajen rashin jin dadin mulkin Shugaba Buhari."

Arewacin Najeriya ta fi kowa shan azabar gazawar Buhari
Arewacin Najeriya ta fi kowa shan azabar gazawar Buhari, Kungiyar Dattawan Arewa Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Ba'a taba samun rabuwar kai tsakanin yan Najeriya ba irin yanzu, Okowa

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, wanda shine mai lakca a taron ya bayyana damuwarsa kan yadda rabuwar kai yayi yawa a Najeriya yanzu.

A cewarsa, ba'a taba samun rabuwar kai tsakanin yan Najeriya irin na yanzu ba a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hotunan Aisha Buhari lokacin da take jiran isowar amaryar dan ta Yusuf Buhari

Yace:

"Najeriya bata taba fuskantar matsalar hadin kai ko rashin yarda da juna irin yanzu ba."

An tabbatar da yadda ‘Yan bindiga suka samu damar shiga makarantar NDA cikin dare

Wata takardar sirri da ta fito daga hedikwatar tsaro na kasa ta yi bayanin yadda ‘yan bindiga suka shiga makarantar sojoji ta NDA, suka yi barna.

Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya bayyana cewa ana tunanin ‘yan bindigan sun shigo makarantar ne ta wani sashe na katanga mara kyau.

Ta titin zuwa filin jirgin sama na Kaduna da ke Afaka, akwai bangaren katangar makarantar sojojin na NDA da shingen da aka sa na wayoyi suna rawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng