Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce yawan mutanen Najeriya ne kan gaba wajen haddasa fitina a kasar
  • A cewarsa, wannan yana taimakawa wajen daukar matasa marasa aikin yi domin aikata laifuka
  • A sakamakon haka, Obasanjo ya ce Najeriya na cikin babbar matsala idan ba za ta iya samar wa matasa aikin yi ba

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilan aikata laifuka a Najeriya.

A cewarsa, ta’addanci, fashi da makami na karuwa a Najeriya sakamakon karuwar yawan mutanen kasar. A zahirin gaskiya, tsohon shugaban kasar ya ce wannan yana hana shi barci cikin dare.

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya
Olusegun Obasanjo yace yawan matasa marasa aikin yi ne matsalar Najeriya Hoto: The Guardian newspaper
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da rahoton kungiyar cigaban Afirka ta 2020 (APG) a Legas mai taken: '' Making Africa’s Population an Asset'', jaridar Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

Obasanjo ya dage cewa dalilin tayar da kayar baya da ta'addanci a kasar bai yi nisa da kasancewar akwai tarin matasa marasa aikin yi da ake daukar su cikin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin masu aikata laifuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“An ce Mohammed Yusuf wanda ya fara Boko Haram mutum ne mai nagarta da sanin yakamata tare da dimbin matasa marasa aikin yi da ke jira domin su saurare shi. Na ji akwai lokacin da ya kira mabiyansa ya ce wa daya, ‘ka je jami’a, shekaru nawa yanzu da ka kammala?’ Ya ce shekara uku kuma me kake yi yanzu? Ya ce, ‘babu aiki.’ Sannan ya amsa, ‘ka ga rashin amfanin ilimin jami’ar ka.”
“Ta haka ne kalmar Boko Haram ta bullo. Ta hanyar mabiyansa ba su da ayyukan yi, ya ce ‘kun ga rashin amfanin ilimin ku na boko.’ Idan ba za mu iya samar da ayyukan yi ga yawan mutanen mu ba, da gaske muna cikin matsala. Babu bukatar wani ya gaya mana wani abu."

Kara karanta wannan

Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci cikin dare

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

A gefe guda, Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, ya ce an fadada rundunar sojojin Najeriya da yawa, duk da cewar tana da karfin samun nasara a yakin da take yi da masu tayar da kayar baya da 'yan fashi a arewacin kasar.

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Babangida wanda ake kira IBB ya bayyana hakan a wata hira da aka watsa a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta, a gidan talabijin na Arise.

Asali: Legit.ng

Online view pixel