Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi korafi a kan hauhawan ta'addanci a kasar
  • Atiku ya bayyana cewa mafita guda da zai kai kasar ga ci gaba shine sake fasalin lamura
  • Ya bayyana cewa duk da cewar akwai rashin tsaro a kasar tunda, lamarin ya kara munana a baya-bayan nan

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi Allah wadai da yawaitar fashi da makami a kasar.

Ya ce ba zai zama abin mamaki ba idan 'yan fashi da masu garkuwa da mutane sun nemi yin rajista tare da Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC) da neman sunayen a jerin Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (NSE), jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar
Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci a kasar inda ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya kuma ce dole ne a sake fasalin Najeriya domin a samu gaggarumin ci gaba cikin hanzari.

Ya ce: "Muna bukatar gyara Najeriya don gujewa afkawa zuwa bala'i."

Abubakar ya yi magana ne a tattaunawar kasa da gabatar da wani littafi mai taken, “Sake gyara Najeriya: Shekaru sittin, muryoyi sittin” a Abuja.

Ya ce:

“Haka ne, an yi garkuwa da‘ yan matan Chibok shekaru 7 da suka gabata.
"Ee, rikice -rikice tsakanin makiyaya da manoma sun kasance tare da mu kafin 2016.
“Amma wa zai yi tunanin cewa ƙasarmu za ta zama mafaka ga masu garkuwa da mutane da kowane irin ɓarayi har ayyukansu na mugunta su zama manyan masana'antu?
“An ba su damar yin aiki a bayyane kuma ba tare da kunya ba ta yadda ba zai ba kowa mamaki ba idan suka nemi yin rajista tare da Hukumar Harkokin Kasuwanci da jera su a Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

“Shekaru biyar da suka gabata, hanyar Abuja zuwa Kaduna ba yanki ne da ba za a iya zuwa ba. Kudu maso Gabas ba yanki ne na yaƙi ba, kuma ba a buƙatar Amotekun don kare rayuka da dukiyoyi a Kudu maso Yamma.
"Waɗannan suna daga cikin bayyanannun shaidu cewa batutuwan da suka kasance tushen littafin da ya kawo mu nan fiye da shekaru biyar da suka gabata sun yi muni."

Tsohon mataimakin shugaban ya ce sake fasalin Najeriya ya zama dole don ganin ci gaba mai dorewa.

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

A wani labarin, tohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilan aikata laifuka a Najeriya.

A cewarsa, ta’addanci, fashi da makami na karuwa a Najeriya sakamakon karuwar yawan mutanen kasar. A zahirin gaskiya, tsohon shugaban kasar ya ce wannan yana hana shi barci cikin dare.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Yi Magana Kan Kashe Musulmai a Jos

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng