Wajibi Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Rage Ciyo Bashi, Sanata Ahmad Lawan

Wajibi Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Rage Ciyo Bashi, Sanata Ahmad Lawan

  • Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, yace ya zama wajibi a nemo hanyar rage ciyo bashin gwamnatin tarayya
  • Lawan ya bayyana haka ne jin kaɗan bayan fitowa daga wata ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa
  • Sanatan ya kuma musanta zargin da ake yaɗawa cewa majalisa ta karbi na goro domin amincewa da PIB

Abuja - Shugaban sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana bukatar rage ciyo bashi daga waje ta hanyar toshe hanyoyin karkatar da kuɗaɗen haraji a ma'aikatun gwamnati, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Lawan ya faɗi hakane a fadar shugaban ƙasa yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaba Buhari.

Shugaban sanatocin yace ya zama wajibi gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su lalubo hanyoyin magance ma'aikatun da basu zuba haraji a asusun gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Wanda Ya Dace Ya Gaji Shugaba Buhari a 2023

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan
Wajibi Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Rage Ciyo Bashi, Sanata Ahmad Lawan Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Me manyan shugabannin suka tatauna?

Sanata lawan yace:

"Mun tattauna abubuwan da suka shafi gwamnati, yadda za'a nemo hanyoyin karin kudaden haraji musamman a matakin kasa, jihohi da kuma kananan hukumomi."
"Akwai ma'aikatun gwamnati da dama dake karkatar da kuɗaɗen haraji ba su zuba su a asusun gwamnati, wannan wata matsala ce da ya kamata a magance ta cikin gaggawa domin muna son rage ciyo bashi."
"Saboda haka idan akwai hanyoyin da zamu samu haraji sosai, hakan zai taimaka mu rage ciyo bashin da muke."
"Duk mun amince da wannan da shugaban ƙasa cewa zamu lalubo hanyar kara inganta tattara haraji."

Kasafin kuɗin shekarar 2022

Shugaban sanatocin ya bayyana cewa sun tattauna kan kasafin kuɗin shekara mai zuwa 2022 da shugaban ƙasa Buhari.

Lawan yace akwai shirin samar da isasshen kaso ga hukumomin tsaro, da kuma wasu ayyuka da aka fara kamar babbar gadar Neja ta biyu, da hanyar Abuja-Kano.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A cewar Lawan sun yi shirin kammala waɗannan ayyukan zuwa shekarar 2022 domin shugaban ƙasa ya kaddamar da su yan Najeriya su amfana.

Shin dagaske majalisa da karbi cin hanci kan PIB?

Sanatan ya musanta zargin cewa majalisa ta karbi dala miliyan $10m domin ta amince da sabon kudirin dokar man fetur PIB.

Ya kara cewa mutane suna magana karangatsai game da shugaban ƙasa, gwamnati da kuma mambobin majalisun tarayya.

"Mutane na kiran mu da sunaye kala daban-daban, kuma kowa yana da damar tofa albarkacin bakinsa amma ina baku shawara ku dinga faɗin alheri."
"Kwanan nan wani yace an baiwa shugaban sanatoci da kakakin majalisar wakilai dala miliyan $10m su rarrabawa abokan aikinsu dan su gaggauta amincewa da kashi 3% ga yankunan dake samar da man fetur."
"Wannan abin dariya ne amma shi dagaske yake, saboda haka inason amfani da wannan damar domin nesanta mu da wannan karyar da ake yaɗawa yan Najeriya don bata sunan wasu mutane."

Kara karanta wannan

Bayan Daukar Alkawari, Fulani Sun Tsamo Masu Garkuwa Daga Cikinsu Sun Mikawa Yan Sanda

A wani labarin kuma Hisbah ta garkame Jarumar Kannywood kan saka al'amuran baɗala a kafar sada zumunta

Hukumar Hisbah ta kulle jarumar masana'antar shirya fina-finai Kannywood , Sadiya Haruna, bisa saka abubuwan baɗala a shafukanta na sada zumunta.

Dailytrust ta ruwaito cewa shugaban sashin kula na hukumar Hisbah, Malam Aliyu Usman, shine ya jagoranci damke wacca ake zargi, mazauniyar Kabuga a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel