Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Wanda Ya Dace Ya Gaji Shugaba Buhari a 2023
- Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace duba da halin da Najeriya ke ciki tana bukatar shugaba ɗan zamani
- Gwamnan yace ya zama wajibi yan Najeriya su yi wa kansu karatun ta natsu wajen zaɓen shugaba a 2023
- Tambuwal Ya kuma yi kira da yi wa hukumar yan sandan ƙasar nan garambawul
Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya bayyana cewa halin da Najeriya ta tsinci kanta ya ta'allaka ne da gazawar gwamnati, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Yace samun kyakkyawan jagoranci kuma idan aka canza fasalin tsaro da kuma tsarin shugabancin kasar nan zai magance kalubalen da ake fama da shi.
Saboda haka gwamnan yace ya kamata yan Najeriya su yi nazari sosai wajen zaɓar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Tambuwal ya faɗi haka ne a yayin gudanar da lakca a wurin taron murnar cikar Mr Richard Akinnola, shekara 63 a duniya da ya gudana a Lagos.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane irin shugaba Najeriya take bukata?
Tambuwal, wanda ya yi lakca mai taken "Kalubalen tsaro a Najeriya da kuma abinda ya jawo wa cigaban kasa," yace Najeriya na bukatar shugaba mai kishi kuma mai ilimin fasaha na zamani.
A jawabinsa, Tambuwal yace:
"Najeriya tana bukatar hazikin shugaba, wanda yake da abokai da makusanta daga kowane lungu da sako na kasar nan."
"Muna bukatar shugaban da baya cin hanci kuma yasan hanyar yaki da cin hanci da rashawa a karan kansa kuma zai iya gina hukumar da zata gagari duk mai son yin magudi."
"Najeriya tana bukatar shugaban ɗan zamani, wanda yasan bukatar amfani da fasahar zamani wajen warware matsaloli."
Najeriya na bukatar shugaban da zai rungumi kowa
Tambuwal ya kara da cewa irin jagoran da Najeriya take bukata shine wanda zai ɗauki kasar kamar mazaɓarsa ya rungumi kowa a matsayin nashi.
"Najeriya na bukatar shugabancin da zai haɗa kan kowa kuma ya kawo dawwamammen zaman lafiya da cigaba ga yan Najeriya."
Sai an gyara hukumar yan sanda
Gwamna Tambuwal ya yi kira da a gyara tsarin hukumar tsaro ta yan sanda, inda yace shugaban ƙasa zai iya kirkirar kudirin ya tura wa yan majalisu.
Yace rundunar yan sandan ƙasar nan ba ta da karfin da ya kamata, shiyasa dole ake tura jami'an soji kowace jiha.
A wani labarin kuma Zamu Iya Yafe Wa Mayakan Boko Haram da Suka Tuba, Amma da Sharadi, Babban Malami
Wani babban malamin coci a Abuja, Rev. Ignatius Kaigama, ya gargaɗi gwamnatin tarayya game da yin gaggawar amincewa da tubabbun yan Boko Haram.
Malamin yace za'a iya yafe wa yan Boko Haram ɗin amma ya kamata gwamnati ta yi adalci duba da yanayin da kasa ke ciki.
Asali: Legit.ng