Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe
- A Arewacin Najeriya, jihar Filato, hukumomi sun ci alwashin zakulo masu tayar da zaune a tsaye a jihar
- Gwamnati ta bayyana cewa, za ta bi dukkan matakai wajen ganin ta kame masu kashe mutane ba dalili
- Hakazalia, gwamnati ta bukaci dubban jama'ar jihar da su ba da hadin kai ga gwamnati a manufarta na wanzar da zaman lafiya
Jos, Filato - Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ce za su bibiyi duk wani mutumin da ya kai hari kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kuma su kama su don fuskantar fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.
Sun kuma ce za su cafke mazauna unguwar ko yankin da abin ya faru don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargi suka tsere.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai a ranar 14 ga watan Agusta a kusa da hanyar Gada-biyu-Rukuba na karamar hukumar Jos ta Arewa da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.
Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Shehu Bala Usman, ya bayyana hakan bayan bitar dokar hana fita da gwamnatin jihar Filato ta kafa.
Shugaban ya ce gwamnatin Gwamna Lalong ta mai da hankali sosai wajen samar da zaman lafiya a yankin, yana mai gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta bari wani mutum ko kungiyoyin da ke da niyyar yin zagon kasa ga kokarin gwamnati su ci ribar barnarsu ba.
Ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta sake lamunta da duk wani aiki da zai haifar da barna da kunci ga 'yan kasa ba, yana mai sake nanata cewa duk wanda aka samu yana da hannu ko da wanene shi za a yi maganinsa a bisa doka.
Don haka, ya yi kira ga shugabannin gargajiya, al'umma, da shugabannin addinai, kungiyoyin ci gaba da matasa da kungiyar ma'aikatan sufurin hanya ta Jos ta Arewa da mutane masu kyakkyawar manufa da su taimaka wa gwamnati wajen wayar da kan mabiyansu.
Ba ma son a kama sunan wani kan kisan musulmai a Jos, Kwamishinan 'yan sandan Filato
Kwamishinan ‘yan sandan Filato, Edward Egbuka, ya ce duk da cewa harin da aka kai kan matafiya a Jos ranar Asabar ba shi ne karon farko da irin wannan lamarin ya faru ba, 'yan sanda ba sa son a kama sunan kowa a lamarin.
Ya lura cewa wadanda suka kai farmaki kan matafiyan a Jos a ranar 14 ga watan Agusta 'yan ta'adda ne da 'yan daba wadanda ke son dagula yanayin tsaro a jihar don haifar da matsala da sace-sace.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Shugaban hukumomin tsaro a jihar ga Gwamna Simon Lalong.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Gwamna Dr Makut Macham ya fitar a Jos, Punch ta ruwaito.
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos
A wani labarin, Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.
Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.
Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.
Asali: Legit.ng