Bayan Daukar Alkawari, Fulani Sun Tsamo Masu Garkuwa Daga Cikinsu Sun Mikawa Yan Sanda a Taraba
- Kungiyar Fulani miyetti Allah ta mika wasu mutum 11 da ake zargin masu garkuwa ne ga hukumar yan sanda
- Kungiyar tace wannan somin taɓi ne a kokarinta na tsame bara gurbi daga cikin fulani a jihar Taraba
- Kwamishinan yan sanda reshen jihar Taraba ya yaba wa fulani tare da tabbatar musu da goyon bayan yan sanda
Taraba - Shugabannin kungiyar Miyetti Allah sun mika mutum 11 da ake zargin masu garkuwa ne ga hukumar yan sanda, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Fulanin sun damka waɗanda ake zargin ne ga kwamishinan yan sandan jihar Taraba, Mista Abimbola Sokoya, a Maraban Kunini, ranar Lahadi.
Legit.ng Hausa ta gano cewa an gabatar da mutanen ne a wurin taron kaddamar da kwamitin mutum 11 da aka kafa domin magance ayyukan ta'addanci, musamman garkuwa da mutane.
Fulani sun fara cika alkawarin da suka dauka
Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Sahabi Tukur, yace wannan wani ɓangaren alkawarin da suka ɗauka ne a gaban sarkin Muri, Alhaji Abbas Tafida.
Sahabi yace:
"Mambobin kwamitin wanda ya kunshe kowane ɓangaren fulani a jihar Taraba, zasu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da jami'an tsaro domin zakulo masu garkuwa da sauran masu aikata laifuka."
Kwamishina ya jinjinawa Fulani
Kwamishinan yan sandan ya yaba wa fulani bisa matakan da suka ɗauka na magance karuwar satar mutane da sauran manyan laifuka.
Ya kuma yi kira da a haɗa karfi da karfe tsakanin jihohin Taraba, Adamawa da Benuwai wajen dakile garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka.
Kwamishinan ya tabbatar wa fulanin cewa hukumarsa zata basu dukkan taimakon da suke bukata wurin zakulo bara gurbin cikinsu.
Wasu sun tuba tare da rantsuwa da Alqur'ani
Hakazalika wasu mutum 6 sun tuba, sannan sun rantse da littafi mai tsarki cewa ba zasu sake aikata duk wasu manyan laifuka da suke yi ba nan gaba.
A wani labarin kuma Ba Ni Na Fara Fadin Wannan Maganar Ba, Gwamna Ya Maida Martani Ga Masu Kiran Ya Yi Murabus
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi watsi da kiran kungiyar arewa (CNG) na yayi murabus sabida yace mutane su kare kansu daga yan bindiga.
Masari yace ba shine gwamnan farko da ya faɗawa mutane su kare kansu daga ta'addancin yan bindiga ba, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng