Hisbah ta garkame Jarumar Kannywood kan saka al'amuran baɗala a kafar sada zumunta

Hisbah ta garkame Jarumar Kannywood kan saka al'amuran baɗala a kafar sada zumunta

  • Hukumar Hisbah ta kame jarumar Kannywood, Sadiya Haruna, bisa zargin yaɗa bidiyoyin baɗala a kafar sada zumunta
  • Hukumar ta kuma gurfanar da Sadiya a gaban kotun shari'ar musulunci dake unguwar Sharada a Kano
  • Alkalin kotun ya yanke wa jarumar hukuncin zuwa islamiyyar Darul Hadith na tsawon wata shida

Kano - Hukumar Hisbah ta kulle jarumar masana'antar shirya fina-finai Kannywood, Sadiya Haruna, bisa saka abubuwan baɗala a shafukanta na sada zumunta.

Dailytrust ta ruwaito cewa shugaban sashin kula na hukumar Hisbah, Malam Aliyu Usman, shine ya jagoranci damke wacca ake zargi, mazauniyar Kabuga a Kano.

Jarumar ta cigaba da zama a hannun hukumar Hisbah har zuwa ranar Litinin da safe, inda aka gurfanar da ita gaban kotun shari'ar musulunci dake zamanta a Sharada.

Jarumar Kannywood, Sadiya Haruna
Hisbah ta garkame Jarumar Kannywood kan saka al'amuran baɗala a kafar sada zumunta Hoto: @sayyada_sadiya_haruna
Asali: Instagram

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa bayan kame Sadiya ne, abokiyar sana'arta a Kannywood, Ummah Shehu, ta nuna fushinta kan lamarin.

Kara karanta wannan

Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaruma Ummah Shehu ta yi barazanar tona asirin wasu jami'an Hisbah da acewarta suke neman mata.

A ikrarin Umma Shehu, Hisbah ba ta da hurumin kame Sadiya Haruna, kasancewar laifi ne wanda idan ma ta aikata tsakanin ta da ubangijinta ne, kuma a cewarta, zai iya yafe mata ya kuma shirye ta.

Wane zarge-zarge aka shigar kan jarumar?

A rahoton farko da aka shigar kan Sadiya, an zarge ta ta saka bidiyoyi da basu dace ba, inda take rawa kuma tana faɗin kalaman batsa.

Hakanan kuma an zargeta da yin rubutun batsa a shafinta na kafar sada zumunta da kuma dandalinta na Youtube.

Sadiya ta amsa laifinta; wane hukunci kotu ta yanke?

Jaruma Sadiya ta amsa laifin da aka karanto mata wanda ya saba wa sashi na 355 na Final kod doka ta 2000.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata

Alkalin dake jagorantar shari'ar, Mai shari'a Ali Jibril Danzaki, ya umarce ta da ta rinka zuwa makarantaar Islamiyya ta Darul Hadith dake Tudun Wada na tsawon watanni shida a matsayin hukuncin laifin da ta aikata.

Alkalin yace shugaban makarantar da kuma hukumar Hisbah su sanya ido a kanta domin tabbatar da tana zuwa islamiyyar kamar yadda kotu ta umarceta.

A wani labarin kuma Zamu Iya Yafe Wa Mayakan Boko Haram da Suka Tuba, Amma da Sharadi, Babban Malami

Wani babban malamin coci a Abuja , Rev. Ignatius Kaigama, ya gargaɗi gwamnatin tarayya game da yin gaggawar amincewa da tubabbun yan Boko Haram.

Malamin yace za'a iya yafe wa yan Boko Haram ɗin amma ya kamata gwamnati ta yi adalci duba da yanayin da kasa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel