2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

  • An ƙarfafa wa matasan Najeriya gwiwar cewa su shirya don jagorantar kasar bayan zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa
  • Wasu manyan jiga-jigan PDP da APC da suka yi taro a Abuja a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, ne suka yi wannan kiran ga matasa
  • Daya daga cikin 'yan siyasar, Sanata Eyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, ya lura cewa lokaci ya yi da matasa za su yi aikin gyara kasar

Abuja - 'Yan siyasar Najeriya daga yankin kudu maso gabas sun yi amanna kan cewa lokaci ya yi da za a bai wa matasa ragamar kula da shugabancin kasa.

Wadanda suka gabatar da wannan ra'ayi a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, yayin wani shiri na Jakadan Matasan Najeriya a kasashen waje (NDYA) wanda aka shirya a Abuja sun hada da Sanata Eyinnaya Abaribe, Rochas Okorocha, da Orji Kalu da sauransu, PM News ta ruwaito.

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari
Yan siyasar sun ce lokaci ya yi da matasa za su shugabanci Najeriya Hoto: Senate
Asali: Facebook

Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya lura cewa ya kamata matasa masu kishi da son gyara batutuwan da ke addabar kowa su dare kujerun shugabanci na gaba.

Sanatan na PDP ya kara da cewa a halin yanzu majalisar kasa na aiki a wani bangare na kundin tsarin mulkin Najeriya don ba matasa damar shiga cikin harkokin siyasa.

Ya ce:

“Majalisar kasa a halin yanzu tana yin bitar kundin tsarin mulki don duba dukkan sassan kundin tsarin mulkinmu da ke bukatar gyara don amfanin kowa.
"Muna kuma duba hanyoyin da za mu ba matasa dama don su shiga a dama da su a shugabancin Najeriya.”

Da yake bayyana ra'ayin Abaribe, Babban bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Kalu, (APC, Abia) ya lura cewa majalisar dokokin Najeriya tana da nasaba da matasa.

Matasan PDP sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP

A wani labarin, matasan jam’iyyar PDP sun yi wa tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, wankin babban bargo akan alakanta jam’iyyarsu da APC, Daily Trust ta wallafa.

Shugabannin jam’iyyar adawar ta PDP sun koka da Jega akan rashin nunawa ‘yan Najeriya gaskiya saboda suna zarginsa da zama daya daga cikin wadanda suka dakatar da cigaban Najeriya tun 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel