Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

  • Ba sabon labari bane cewa dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf, na shirin auren gimbiyar Kano
  • Za a kulla auratayya tsakanin Yusuf da diyar sarkin Bichi a Kano, Gimbiya Zahra Bayero, a ranar 21 ga Agusta, 2021
  • Tuni dai aka fara shagulgulan bikin inda aka yi wankan amarya
  • Sai dai kuma yanayin shigar Amarya Zahra sun bar baya da kura domin mutane da dama sun ga rashin dacewar hakan

Ana shirin yin wani gagaruin biki a Najeriya tsakanin iyalan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na masarautar Bichi da ke jihar Kano.

Dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari, zai angwance da muradin ransa, Zahra Bayero a ranar 21 ga watan Agusta, 2021. Sai dai tuni aka fara shagulgulan biki inda aka yi wankan Amarya.

Jama'a na cece-kuce a kan yanayin shigar Zahra Bayero a wajen taron wankan amarya
Jama'a sun ce shigar bai dace da 'yar gidan sarautar arewa ba Hoto: @trendjournalng, @fabricblogger
Asali: Instagram

A hotunan shagalin da shafin northern_hibiscuss ya wallafa a Instagram an gano Amarya Zahra cikin kwaliyya da doguwar riga fara irin ta turawa, sannan amaryar bata yane kanta da kallabi ba.

Yanayin shigar tata ta sanya mabiya shafin tofa albarkacin bakunansu, inda hakan bai yi wa wasu da dama dadi ba.

Da yawa sun ce wannan abu da aka yi a wajen taron ba al’adar mallam Bahaushe bane musamman ma ace wanda ya fito daga babban gida irin na masarautar Bichi.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin da mabiya shafin sadarwar suka yi a kasa:

young_ustaax ya ce:

“Da a bikin masarauta har Alkyabba aje sawa cikin sutura gwanin ban sha’awa Amma masarautar ma yanzu an koma E’ yane duk harkar dayace tunda yanzu sun bar tafarkin Shehu Usman Danfodio... Allah ya bama Yusuf da zarah zaman lafiya, da zuri’a na gari.”

sadia_nas ta yi sharhi cewa:

“Sai mun sake jaddada maganar saka kallabi, ba burgewa ba ce kina diyar Sarkin gargajiya kuma masarautar musulunci kiyi kama da wata qabila kuma wani addini, wannan kahirci ya ishe mu, mun ji an sa gown idan kin sa kallabi mutuwa zaki yi?? sai ma kin fi kyau wallahi, saboda qin Allah wai a ce duk zuri’arku duk fadin masarautar Kano an rasa Iyayen da zasu tursasa ki kiyi shigar kirki. Diyar babban gida kuma gidan sarauta amma babu magaya. Wannan ba wakilci mai kyau bane ga matan arewa musulmai.”

_gbenterprises ta ce:

“Dole mutanen Kudu suche Shariar mu ta musulunci akan talakawa take aiki kadai, na Rantse da Sarkin da ke busamin numfashi da yar Takalaka ko wani ordinary citizen ce tayi shiga haka da sai anyi chaaa akanta wata kila har Malam Abdullahi Gadon Kaya sai yayi Huduba akanta !!! But she's royal and Elite so its "Awwwn" "she's cute" Allah ya bada Zaman Lafiya.”

wrash_kitchenutensils ta ce:

“Allahummarzuqni taubatan nasuha qablal mauti. Allah ka karemu ka kare mana daga sharrin zamani”

sweet_meenah ta yi martani:

“Shin ‘yan hisbah na yajin aiki ne a Kano. Kawai dai ina tunani ne.”

fashminadik_enterprise ta ce:

“Hm saidai kawai fatan alheri ,amman muna cikin damuwa a arewa,wai yar sarki kenan na hausawa musulmi.Allah ya shirye mu baki daya.”

A baya mun kawo cewa alamu bayyane suke na cewa tuni aka fara shagalin bikin gidan shugaban kasa da na gidan sarautar Bichi.

Tun a ranar Asabar da ta gabata Legit.ng ta fara kawo muku kyawawan hotunan wasan Polon da aka yi a ranar Juma'a da ta gabata na bikin diyar Sarkin Bichi, Gimbiya Zahra Bayero da dan shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel