Abun bakin ciki: Tsohon sanatan Najeriya ya rasu bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya

Abun bakin ciki: Tsohon sanatan Najeriya ya rasu bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya

  • Gwamnatin jihar Neja ta bayyana kaduwa kan rasuwar mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya mai ritaya, Nuhu Aliyu
  • Ana yiwa Aliyu wanda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a majalisar dattawa kallon dattijo mai daraja
  • Marigayin sanatan yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar Peoples Democratic Party a jihar Neja

Jihar Neja - Nuhu Aliyu, tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a majalisar dattawa, ya rasu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Aliyu wanda ya kasance mataimakin sufeto janar na 'yan sanda mai ritaya ya rasu a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 79 a duniya.

Abun bakin ciki: Tsohon sanatan Najeriya ya rasu bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya
Aliyu ya kasance tsohon mataimakin sufeto janar na 'yan sanda Hoto: Ceceko Usman
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da mutuwar tsohon dan majalisar.

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana rasuwar Aliyu a matsayin babban rashi.

Matane ya ce:

''Kishin kasa da kyakkyawar riko wajen gudanar da ayyukan majalisa game da jin dadin jama'a da marigayi Sanata Nuhu Aliyu ya nuna sun cancanci ayi koyi da su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata

"Amma dole ne mu rarrashi zuciyarmu cewa daga Allah muke kuma gare Shi duk za mu koma. Babu wanda zai rayu fiye da lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya diban masa.”

Wata majiya daga ahlinsa ta shaida wa jaridar This Day cewa za a yi jana’izar dan sandan mai ritaya a makabartar Barnawa da ke Kaduna da misalin karfe biyu na ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Marigayi dan siyasar ya kasance jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party na farko a jihar Neja kafin a zabe shi a majalisar dattijai a 1999 sannan aka sake zabar shi kan wannan matsayi a 2003 da 2007.

A wani labari na daban, wasu da ake zargin yan ƙungiyar daba ne sun kashe ɗalibin kwalejin fasaha ta jihar Kwara mai suna, Olawale.

Dailytrust ta ruwaito cewa yan daban, waɗanda suke ƙungiyar adawa, sun farmake shi ne jim kaɗan bayan ya bar gida ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Yadda Gwamna Buni da Minista su ka sabawa umarnin Mataimakin Shugaban kasa

An gano kan ɗalibin a shataletalen Unity a Ilorin bayan mahaifiyarshi ta shafe awanni tana neman ɗan nata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel