Matasan PDP sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP

Matasan PDP sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP

  • Jagororin matasan jam’iyyar PDP sun caccaki Farfesa Attahiru Jega bisa kwatanta jam’iyyarsu da jam’iyya mai mulki (APC)
  • A cewar matasan, Jega yana daya daga cikin ‘yan Najeriyan da suka mayar da kasar nan baya tun shekarar 2015
  • A wata takarda wacce shugaban jam’iyyar PDP, Injiniya Salaudeen A. Lukman yasa hannu yayi wa Jega wankin babban bargo

Matasan jam’iyyar PDP sun yi wa tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, wankin babban bargo akan alakanta jam’iyyarsu da APC, Daily Trust ta wallafa.

Shugabannin jam’iyyar adawar ta PDP sun koka da Jega akan rashin nunawa ‘yan Najeriya gaskiya saboda suna zarginsa da zama daya daga cikin wadanda suka dakatar da cigaban Najeriya tun 2015.

Matasa sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP
Matasa sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Me matasan suka ce?

A wata takarda wacce shugaban jam’iyyar na kasa, Salaudeen A. Lukman ya sanya hannu, matasan PDP sun nuna takaicin su akan maganganun da tsohon shugaban INEC din yayi a BBC akan zargin ko dai da gangan yake yi don ya rudar da jama’a ko kuma salo ne na tallata sabuwar jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan

Rigimar cikin gidan PDP ta kara cabewa, wasu shugabanni na barazanar murabus kwanan nan

Abin ban takaici ne ace wanda yake da hannu wurin sanya Najeriya da ‘yan Najeriya a cikin halin da take ciki na talauci, yunwa, fatara da rashin tsaro ya budi baki yana irin wadannan maganganun.
Mutum zai yi mamaki akan yadda sannanne Farfesa a harkar siyasa kuma wanda ya girmi ita kanta Najeriya tare da samun gogewa ta fannoni da dama ya budi baki yana wannan soki-burutsun.
Ko dai da gangan yake yi don ya rudar da jama’a ko kuma yana so ya sakawa jama’a ra’ayin sabuwar jam’iyyarsa wacce hakan ba daraja, mutunci ko kuma dacewa bane hakan akan mutum mai daraja irin Farfesa Jega ganin cewa shi tsohon shugaba ne na INEC.
A ce a zamanin mulkin PDP da Goodluck Jonathan yaje ya zabo dan arewa, musulmi, dan garin Jega dake jihar Kebbi, wanda yake koyarwa a jami’ar Bayero dake Kano musamman ya daura shi a matsayin shugaban INEC, hakan kadai ya isa ace kowa ya musanta batun Jega na hada APC da PDP.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

Jam’iyyar da ta bunkasa tattalin arzikin kasar nan a kasashen Afirka lokacin ana canja N160 ga kowacce dala daya sannan kowacce litar mai ta zama N87 kuma yake hada mulkinta dana APC da ta mayar da Najeriya daya daga cikin kasa mafi talauci yayin da darajar duk dala daya ta zama N510 ga bala’in tsadar rayuwa da kashe-kashe da masu garkuwa da mutane da suke bin mutum har gida.
Sannan yanzu cin hanci da rashawa sun yi katutu bayan bayyanar kungiyar Boko Haram wacce ta addabi kasar nan gabadaya.

Jega ya fito ya baiwa 'yan Najeriya hakuri

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, matasan sun ce don haka wajibi ne tsohon shugaban INEC din ya fito ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri akan yadda ya tsaya tsayin daka ya kawo APC mulki.

Don haka ‘yan Najeriya suyi watsi da maganganun Farfesa Jega da soki burutsunsa, tabbas akwai lauje cikin nadi don akwai alamar hajarsa yake so ya tallata.

Kara karanta wannan

A karshe tsohon Shugaban INEC ya yi watsi da APC da PDP, ya shiga PRP, ya bayyana dalilai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng