Mun rabu da mahaifiyata lafiya, Mawaki Ala yace yayin da yake zubda hawaye

Mun rabu da mahaifiyata lafiya, Mawaki Ala yace yayin da yake zubda hawaye

  • Jama’a sun yi tururuwa wurin halartar jana’izar mahaifiyar mawaki Ala wadanda suka hada da malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan fim, ‘yan siyasa da sauransu
  • An yi jana’izar Hajiya Bilkisu a gidan danta Alan waka da misalin karfe 9:06 na safe a unguwar Maidile kamar yadda rahotonni suka bayyana
  • Dimbin al’umma sun raka gawar zuwa makwancinta a makabartar dake Tarauni cike da alhini sakamakon yadda kowa ya ga danta cikin matsananciyar damuwa

Kano - Manyan malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan film, mawaka da sauran daukacin al’ummar musulmi sun yi tururuwa wurin halartar jana’izar mahaifiyar Aminu Ala, shahararren mawakin nan da misalin karfe 9:06 na safiyar jiya a gidansa dake unguwar Maidile.

Kammala jana’izar ke da wuya aka tattara zuwa kaita makwancinta dake makabartar tarauni. Bayan kammala hakan ne mujallar fim ta tattauna da Ala don jin ta bakinsa inda yace:

Dukkan rai mamacine kuma yana jiran ranar mutuwarsa don haka ta koma ga mahaliccinta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

KU KARANTA: Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda

Mun rabu da mahaifiyata lafiya, Mawaki Ala yace yayin da yake zubda hawaye
Mun rabu da mahaifiyata lafiya, Mawaki Ala yace yayin da yake zubda hawaye. Hoto daga @alan_waka
Asali: Instagram

KU KARANTA: Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe

Na rabu da mahaifiyata lafiya inji Alan waka

Yayin da aka kammala rufe mahaifiyar Ala a makwancinta sai Ala yace:

Muna mika godiyarmu ga ubangiji mahalicci da ya rabamu da duka iyayenmu lafiya, da mahaifina Sharif Adamu Maidoki da Mahaifiyata Hajiya Bilkisu Adamu.
Mun zauna lafiya da ita cikin so da kauna da amana kuma Allah ya rabamu lafiya, tana tsananin yabona da ‘yan uwana kuma duk ‘yan uwanta suna alfahari da ita.
Mahaifiyata mai zumunci ce don ko kwana biyu da suka gabata sai da ta kai ziyara taje duba mara lafiya a asibiti, wanda hakan yayi sanadiyyar rikicewar jikinta. Tayi fama da hawan jini na fiye da shekaru arba’in kuma mai kula da kiyaye dokokin asibiti ce.

Kara karanta wannan

Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

Godiyar Ala ga masoya da suka halarci jana'izar mahaifiyarsa

Ala ya mika sakon godiyarsa ga duk wadanda suka halarci jana’izar da ma wadanda basu samu dama ba. Inda yace:

Hakika masoya sun nuna min soyayya da halacci kuma hakan ya nuna ana zaune lafiya ne musamman abokan sana’a da iyaye.

Mai Shari'a Garba, babban alkalin FCT yayi murabus, ya bayyana dalili

Sabon babban alkalin FCT, Justice Salisu Garba ya yi murabus da kanshi bayan an nadashi a matsayin mai gudanarwa na NJI.

An samu wannan sanarwar ne a wata takarda wacce hadimin CJN na fannin yada labarai, Ahuraka Isah ya gabatar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewarsa, NJIBG, Karkashin shugabancin babban alkalin Najeriya, CJN, Justice Tanko Muhammad, ta amince da nadin Garba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel