Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda

Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda

  • Hadakar rundunonin sojin kasa da na kasa sun ragargaji ‘yan Boko Haram da dama dake yankin Gubio a jihar Borno
  • Kamar yadda wani jami’in binciken sirri ya tabbatar, sojojin saman sun yi ta harbi ta sama suka kone miyagun makamai ‘yan ta’addan
  • Bayan jin aman wuta ta sama, ‘yan ISWAP din sun fara tserewa take a nan sojojin kasa suka bude musu wuta suka karkashe su

Gubio, Borno - Hadakar rundunonin sojin kasa da na sama sun ragargaji ‘yan ta’addan Boko Haram-ISWAP a wuraren Gubio dake jihar Borno.

Wani jami’in binciken sirri ya sanar da PRNigeria cewa a kalla motocin yaki hudu sojojin sama dana kasa suka lalata yayin ragargazar ‘yan ta’addan.

KU KARANTA: Hotunan ango da yayi wuff da zuka-zukan amare 4 a rana daya sun janyo cece-kuce

Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda
Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Dalla-dalla: Yaya al'amarin ya faru?

Lamarin daya faru ne a ranar Litinin ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan ta’addan da dama.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno

PRNigeria ta fahimci yadda rundunar sojin kasa suka fuskanci ‘yan ta’addan yayin da jirgin sojojin NAF kuma ya fita wani aikin na daban aka umarce shi da ya cigaba da aiki a wuraren Gubio.

Bayan jirgin NAF ya hango ‘yan Boko Haram suna yawo da motocin yakinsu guda hudu take anan suka fara auna musu harbi ta sama daga nan suka dakatar dasu.
Bayan harbe-harben, wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun so su tsere amma take a nan sojojin kasa suka kashesu.
Baya ga lalata motocin yakinsu, an samu miyagun makamai daga hannunsu kamar bindigogi masu jigida, harsasai, jarkoki, tabar wiwi, magungunan inganta jima’i, littattafai wadanda akwai hanyoyin hada bama-bamai da sauransu,” a cewarsa.

Ina 'yan ta'adda suka nufa bayan jin ruwan wuta?

Bayan wadannan rahotonnin an samu labarin yadda ‘yan ta’addan suka fara tafiya tsakanin Sambisa zuwa Parisu zuwa yankin Njimiya yayin da wani jirgin saman yayi gaggawar ragargazar ‘yan Boko Haram din.

Kara karanta wannan

Danmaraki, Sama'ilo da wasu shugabannin 'yan bindiga sama da 20 na neman rangwame

Yayin da aka tambayi kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya sanar da PRNigeria cewa harin da suka kai ya haifi da mai ido.

Ba zan iya bayar da bayanai akan lamarin da ya faru a ranar Litinin ba, sojojin sama sun samu nasarar lalata motocin yakinsu yayin da sojojin kasan suka ragargaji ‘yan ta’addan da suke kokarin tserewa.

Kwamandan sojin, Janar Christipher Musa ya yabawa rundunar sojin akan kokarin da sojojin kasa dana sama suka yi na ragargazar ‘yan ISWAP-Boko Haram din a maboyarsu.

KU KARANTA: Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki

IGP ya maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya nada DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban bangaren binciken sirri na 'yan sanda (IRT).

Disu zai maye gurbin Abba Kyari, wanda ake zarginsa kan wata harkallar cin hanci da gagarumin dan damfarar yanar gizo da Amurka ta cafke, Ramon Abbas.

Kara karanta wannan

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe Sojojin kasar Kamaru a wasu sababbin hare-hare

Frank Mba, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Najeriya yace an nada Disu a wata takarda da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel