Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party ta fara shirin hada kan dukkan fusatattun mambobinta
  • Kola Ologbodiyan, sakataren jam’iyyar PDP na kasa, ya sanar da hakan a wani bidiyo na Facebook a ranar Talata, 3 ga watan Agusta
  • Ologbodiyan ya ce kafa tsarin warware rikicin wani bangare ne na shawarar da jam'iyyar ta yanke a wani taro a ranar Talata

A kokarinta na kawo karshen rikicin da ke barazana gare ta, jam'iyyar PDP a yayin taron ta na gaggawa a Abuja a ranar Talata, 3 ga watan Agusta, ta yanke wasu muhimman shawarwari.

A cikin wani bidiyon Facebook na PDP, kakakin jam'iyyar adawa ta kasa, Kola Ologbondiyan, ya sanar da wasu shawarwari da aka yanke cikin gaggawa.

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara
Jam'iyyar PDP ta sha alwashin sasanta fusatattun 'ya'yanta Hoto: PDP
Asali: Facebook

Ologbodiyan ya bayyana cewa PDP za ta duba korafe -korafen da mambobin Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) da na Majalisar Zartarwar jam’iyyar ta Kasa (NEC) suka gabatar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Manyan Shugabannin PDP Na Kasa 7 Sun Yi Murabus

Ya kuma bayyana cewa an hanzarta yin amfani da wata hanyar warware rikicin cikin gida don magance matsalolin da ke kasa.

Kakakin jam’iyyar ya ce PDP na kira ga duk masu ruwa da tsaki da membobin da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu yayin da suke magance matsalolin baki daya.

Manyan jami’an jam’iyyar PDP na kasa 7 sun yi murabus daga mukamansu

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa jami’an jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa su bakwai sun yi murabus daga mukamansu.

Manyan jiga-jigan jam'iyyar sun bayyana hakan ne a cikin wasiku daban-daban da suka aika wa sakataren jam'iyyar na kasa a ranar Talata, 3 ga watan Agusta.

Sun yi zargin cewa shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus ya yi masu rashin adalci, Channels Television ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel