Mai Shari'a Garba, babban alkalin FCT yayi murabus, ya bayyana dalili
- Babban alkalin FCT, Justice Salisu Garba, ya yi murabus da kanshi tun bayan nadin da aka mishi a matsayin mai gudanarwa na NJI
- An samu wannan labarin ne a wata takarda wacce hadimin CJN din, Ahuraka Isah ya gabatar a ranar Litinin
- Kamar yadda takardar ta tabbatar, Justice Garba ya yi murabus ne da kansa tun bayan samun wannan mukami
Sabon babban alkalin FCT, Justice Salisu Garba ya yi murabus da kanshi bayan an nadashi a matsayin mai gudanarwa na NJI.
An samu wannan sanarwar ne a wata takarda wacce hadimin CJN na fannin yada labarai, Ahuraka Isah ya gabatar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.
A cewarsa, NJIBG, Karkashin shugabancin babban alkalin Najeriya, CJN, Justice Tanko Muhammad, ta amince da nadin Garba.
KU KARANTA: Da duminsa: An dage zaben kananan hukumomi na jihar Kaduna, an saka sabuwar rana
Justice Garba, wanda shine babban alkalin FCT har zuwa lokacin da yayi murabus zai cigaba da aiki a NJI.
An rantsar dashi a matsayinsa na babban alkalin FCT a ranar 7 ga watan Yuni kuma ya kamata yayi murabus ne a ranar 10 ga watan Oktoba lokacin da zai cika shekaru 65.
An haifi Garba ne a ranar 10 ga watan Oktoban 1956 a karamar hukumar Malumfashi dake jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.
An rantsar dashi a matsayin lauya a 1984 kuma ya kammala bautar kasarsa a 1985. Ya cigaba da aikinsa a matsayin lauya na tsawon shekaru 3 bayan bautar kasarsa.
An nada shi a matsayin alkalin kotun majistare dake Abuja a 1989 sannan ya yi aiki a matsayin rijistira a babbar kotu dake Abuja a 1998.
KU KARANTA: Hotunan ango da yayi wuff da zuka-zukan amare 4 a rana daya sun janyo cece-kuce
Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki
Usman Kyari, kanin Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda, ya zama a saman kanun labarai bayan jama'a sun kyalla ido sun ga irin hotunan rayuwarsa da yake wallafawa a shafinsa na Instagram.
Hankali ya koma kan Usman ne bayan Hushpuppi, wanda aka fi sani da Ramon Abbas, ya ce ya baiwa Abba Kyari wasu makuden kudaden domin ya kama wani dan damfara abokin hamayyarsa.
Kafin aukuwar wannan lamarin, an san babban dan sandan da zama koyaushe a kafar sada zumunta ta Instagram.
Asali: Legit.ng