Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

  • Buba Marwa, Shugaban NDLEA ya umarci jami’an tsaro da su mutsuke duk wasu masu safarar miyagun kwayoyi a fadin Najeriya
  • Ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba a wani taron karin girma ga manyan jami'ai a ranar Alhamis a Abuja
  • Ya kara da bayyana yadda shugaba Buhari yake basu goyon baya dari bisa dari wurin cimma manufarsu

FCT, Abuja - Buba Marwa, shugaban NDLEA ya umarci jami’an tsaro da su ragargaji masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Marwa ya yi wannan maganar a ranar Laraba yayin wani taro na kara wa manyan jami'an NDLEA girma a ranar Alhamis a Abuja.

A cewarsa wannan salo ne na musamman na yaki da harkar miyagun kwayoyi a kasar nan kuma hakan da alamu zai cimma nasara, TheCable ta ruwaito.

KU KARANTA: Ango dake aiki kan na'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce

Kara karanta wannan

Buhari ya sha alwashin kara kasafin ilimi da kashi 50% a cikin shekaru 2

Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma
Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya sha alwashin kara kasafin ilimi da kashi 50% a cikin shekaru 2

Buba Marwa yace wannan yaki ne na musamman

Wannan yaki ne wanda wajibi a dage akan shi, gaba daya sai an bincike kasar nan kuma zamu samu nasara.
Don haka ina umartar duk ma’aikatan da suke karkashina da su dage wurin ragargazar masu safarar miyagun kwayoyi a kowanne bangare na kasar nan.

Shugaban NDLEA ya kara bayyana nasarorin nan sakamakon bayar da gudunmawar da shugaba Buhari ya bayar.

A cewarsa shugaba Buhari ya dage wurin taimaka wa ma’akatan da suke karkashin ma’aikatarsa, TheCable ta ruwaito.

Marwa ya tabbatar wa da ma’aikatan NDLEA cewa zai tabbatar da walwala da jin dadinsu.

Miyagu sun sheke dan takarar karamar hukuma na Kaduna

Dan takarar jam'iyyar All Progressive Chairmanship Congress (APC) na karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna, Alamkah Dominic Usman wanda aka fi sani Cashman ya sheka lahira bayan wasu miyagun 'yan bindiga sun harbe shi a jihar Benue.

Kara karanta wannan

Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

A yayin zantawa da Daily Trust, shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Kachia, Alhaji Ahmed Tijjani Sulaiman, ya ce an harbe Usman a wani wuri a jihar Benue.

Alhaji Sulaiman ya ce, Usman amintaccen dan jam'iyya ne kuma ya hadu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Binuwai inda iyalinsa ke zama, bai san cewa yana dab da amsa kiran ubangijinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel