Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe

Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe

  • Shahararren dan siyasa kuma mai neman kujerar gwamnan Kano, A.A Zaura ya sha alwashin gina Film Village idan ya ci zabe
  • Ya sanar da hakan ne ta bakin jarumi T.Y Shaban a yayin da ake tantance matasa kan gasar da gidauniyar Zaura ta saka
  • Dan siyasan ya saka gasar bidiyo na waka inda zai baiwa masu nasara 30 kyautuka da suka hada da mota, adaidaita da babura

Kano - Fitaccen dan siyasa kuma mai neman kujerar gwamnan Kano, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim wanda aka fi sani da A.A. Zaura ya dauka alkawarin gina tsangayar shirya fina-finai wacce ake kira da Film Village matukar burinsa ya cika.

Wannan busharar ga jaruman masana'antar Kannywoood ta fito ne daga bakin jarumi T.Y Shaban a wurin wani taro da aka yi na tantance matasa da suka shiga gasar wakar bidiyo ta gidauniyar A.A Zaura, Mujallar Fim ta ruwaito.

KU KARANTA: Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe

Read also

Rikicin APC: Yadda Gwamna Buni da Minista su ka sabawa umarnin Mataimakin Shugaban kasa

Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe
Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe. Hoto daga dailynigerian.com
Source: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: An dage zaben kananan hukumomi na jihar Kaduna, an saka sabuwar rana

Jawabin T.Y Shaban kan gasar

A cewara T. Y Shaban:

Wannan dama ce da muka samu inda aka budeta tsakanin matasa mata da maza da kuma masu bukata musamman a fannin shirya waka inda za a dauka bidiyo da bai zarce minti 1 da rabi ba.
Duba da yadda a zamanin nan matasa suke baiwa bangarorin nishadi muhimmanci yasa aka yi shawarar kirkiro wannan gasa. Ita ce irinta ta farko da za a bai wa wadanda aka zaba kyautuka tun daga wanda ya zo na 1 har na 30. Matasa kimanin 3,000 ne suka shiga.

Kamar yadda jarumi Shaban wanda yake daya daga cikin alkalan gasar ya sanar, ya ce suna lura da wasu ka'idoji 9 na dole da mutum sai ya cika kafin nasara.

Muna kokarin gina tsangayar shirya fina-finai

A yayin da mujallar Fim ta so jin ko akwai abinda zai kawowa masana'antar cigaba ta hannun gidauniyar, Shaban ya ce:

Read also

Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

Muna kokari tare da shugaban wannan gidauniyar, Alhaji Abdulsalam Abdulkarin wurin fito da tsare-tsare da zasu taimakawa jarumai da ma wadanda ke sha'awar shigowa masana'antar ta hanyar gina Film Village.

Kyautuakan da za a baiwa masu nasara a gasar

Daga cikin kyautukan da za a baiwa wadanda suka yi nasara a gasar gidauniyar A.A Zaura sun hada da mota, adaidaita sahu, babura, keken hawa da kuma kudade.

Source: Legit

Online view pixel