Ba a kama ni ba: Saraki ya magantu kan batun kasancewarsa a hannun EFCC
- Abubakar Bukola Saraki ya bayyana gaskiyar abin da ya faru a hukumar EFCC da ya ziyarta
- A cewarsa, ba kame shi aka yi ba, yana mai bayyana cewa, shi da kansa ya mika kansa ga hukumar
- Ya kuma bayyana cewa, ya warware dukkan abubuwan da ake bukata ya warware kuma a shirye ya je hukumar
Abuja - Abubakar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa na Najeriya ya bayyana gaskiyar abin da ya faru lokacin da ya kasance a hukumar EFCC da yammacin jiya Asabar, 31 ga watan Yuli, 2021.
Saraki, ya bayyana cewa, ba kama shi aka yi ba, kawai dai ya kai kansa ne domin fayyace wasu batutuwa da suka taso game dashi.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, dauke da sa hannun Yusuph Olaniyonu, na ofishin yada labarai na Saraki ya bayyana cewa, Saraki ya kai kansa ofishin EFCC da son ransa, kuma ba kama shi aka yi ba.
Da yake bayyana wani batu, wani yankin sanarwar ya ce:
"Za a tuna cewa daidai da umurnin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan karar Hakkin Dan Adam da Dakta Saraki ya shigar a lokacin tsohon Shugaban Hukumar EFCC wanda ya hana hukumar binciken sa har sai an warware lamarin.
"Hukumar a zaman ta na karshe a ranar 14 ga Yuli, 2021, ta roki alkalin cewa umurnin yana hana su yin aikin su.
"Bayan wannan korafi, Dakta Saraki, a matsayinsa na dan kasa mai rikon amana, a cikin son ransa ya tunkari hukumar a farkon lokacin da ya dace, cikin shiri ya ziyarci ofishin hukumar tare da fayyace dukkan batutuwan da za su so su gabatar.
"Don haka, ya ziyarci ofishin hukumar a yammacin yau kuma ya amsa wasu tambayoyi.
"Dakta Saraki ya kuma tabbatar wa da hukumar cewa ba shi da abin da zai boye kuma a ko yaushe zai mika kansa don fayyace duk wasu batutuwa da ka iya bukatar bayaninsa.
Saraki na hannunmu, Hukumar EFCC ta tabbatar da damke tsohon shugaban majalisar dattawa
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC a ranar Asabar a Abuja ta tabbatar da damke tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN cewa an gayyaci Saraki ne domin yi masa tambayoyi kan zargin almundahana da babakeren wasu kudade.
Ya ce Saraki yanzu haka na hannunsu kuma suna yi masa tambayoyi. Mun kawo muku cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta tsare tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, bisa zargin sata da handame kudade.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an tsare Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara a ranar Asabar, majiyoyin da suka shaida hakan sun ce, lamarin ka iya haifar da wani tashin hankali ga dan siyasar.
An damke Tanko Al-Makura
Labarin damke Saraki ya biyo bayan damke tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, da uwargidarsa Mairo.
Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaida cewa jami'an EFCC sun yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja kan zargin rashawa.
Amma Tanko Al-Makura ya karyata jita-jitan dake yawo inda yace hukumar ta gayyace shi ne kan wasu korafe-korafe da ake akansa, inda ya yi tattaki yaje ofishin hukumar ya gana da shugabanta da wasu jami'anta cikin kankanin lokaci.
Asali: Legit.ng