Sanata Al-Makura ya karya jita-jitan cewa EFCC ta kame shi da matarsa, ya yi bayani

Sanata Al-Makura ya karya jita-jitan cewa EFCC ta kame shi da matarsa, ya yi bayani

  • Sanata Tanko Al-Makura ya karya jita-jitar cewa, hukumar EFCC ta kame shi da matarsa
  • Ya bayyana dalilin zuwansa ofishin hukumar ta EFCC, sannan ya yi bayani dalla-dalla
  • Hakazalika ya bayyana yiyuwar wasu zarge-zarge kan neman shugabancin jam'iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura ya karyata jita-jitan dake yawo cewa, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi ram dashi tare da matarsa.

A jiya ne 28 ga watan Yuli jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, jami'an hukumar EFCC sun kame sanatan hakazalika sun hada da matarsa sun tafi dasu bisa zargin cin hanci da rashawa.

Amma a cewar Al-Makura, hukumar ta gayyace shi ne kan wasu korafe-korafe da ake akansa, inda ya yi tattaki yaje ofishin hukumar ya gana da shugabanta da wasu jami'anta cikin kankanin lokaci.

Sanata Al-Makura ya karya jita-jitan cewa EFCC ta kame shi da matarsa, ya yi bayani
Sanata Tanko Al-Makura | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Al-Makura yayin wata hira da BBC Hausa ya bayyana jin mamaki game da jita-jitar inda yake cewa:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa

"Wannan jita-jita ta ba ni mamaki, ta ba mutane da dama mamaki."

Ya ce dama hukumar ta EFCC ta gayyace shi tun kafin Sallah amma ya shaida masu cewa ba zai samu damar amsa gayyatar ba sai bayan Sallah, shi ya sa kuma ya shirya ya je don jin dalilin gayyatar.

Sanata Al-Makura ya kara da cewa:

"Ko da na je na gana da shugaban hukumar, sai ya sanar da ni cewa dama korafe-korafe ne da mutane ke yi a kaina, kuma ana son a ji ta bakina. Ganawata da shugaban EFCC duka ba ta wuce minti goma ba."

Kamar yadda wasu masu yada jita-jitar ke cewa, kama shi na da alaka da neman takarar shugabancin jam'iyyar APC, Al-Makura ya kuma karyata wannan batu.

Ya ce:

"Masu wannan maganar na yi ne don dakushe neman kujerar shugabancin APC na kasa da mutane da dama ke so in yi. Sai dai ni ba ni da damuwa da kowa."

Kara karanta wannan

Na gwammace in mutu da na bai wa Fulani filin kiwo, in ji wani Gwamna

Ya ce mai yiwuwa akwai masu wata manufa a gare shi sabanin wanda masoyansa ke da shi a kansa.

Sanata Al-Makura ya ce shi dan Najeriya ne mai bin dokar jam'iyya, shi ya sa ma bai dage wajen yakin neman shugabancin jam'iyyar APC ba.

Ya kara da cewa:

"Na tsaya ne saboda a matsayina na dan jam'iyya mai bin umarnin shugabannin jam'iyya, na jira ne in ji irin ka'idojin da za su sa da inda jam'iyyar ta dosa kafin in bude fagen neman shugabancin jam'iyyar."

EFCC ta daskarar da asusun bankin 'yar majalisa bayan ta siya motar N1bn

Daga cikin binciken siyan motocin da majalisar jihar Oyo tayi, hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi da asusu na majalisar jihar.

Tribune Online ta ruwaito cewa EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi ta majalisar wacce ta ki amsa gayyatar da hukumar tayi mata.

Kara karanta wannan

Tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya Ta Bayyana Cutar Dake Damunta Yasa Aka Ji Ta Shiru

Daskarar da asusun bankin na hana mutum cire kudi daga asusun bankinsa gaba daya.

Majalisar a Zamfara ta nemi matamakin gwamna ya bayyana a gabanta cikin sa'o'i 48

A wani labarin daban, Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta ba Mataimakin Gwamna, Barista Aliyu Mahdi Gusau, wa’adin sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta kan zargin aikata ba daidai ba a hukumance, Channels Tv ta ruwaito.

Zai bayyana a gaban majalisar ne kan wani taron siyasa da aka gudanar a ranar 10 ga watan Yuli, yayin da 'yan bindiga suka kai hare-haren kan al'ummomin Maradun a daidai lokacin da ake taron.

Karin wa’adin ranar Talatan ya biyo bayan kudirin da Mataimakin Shugaban majalisar, Nasiru Bello Bungudu ya gabatar don bayyana dalilin da ya sa ya gudanar da taron siyasa a yayin da kashe-kashen da suka faru a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.