Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

  • Limamin Katolika na Sokoto Diocese, Matthew Kukah, ya nuna damuwa game da kalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu
  • Shugaban addinin ya bayyana dalilin da ya sa matasan Najeriya ke ganin gaba daya sun zama marasa karfi da abubuwan da ke faruwa a kasar
  • Bishop din ya bukaci ‘yan kasar da su tsunduma cikin dimokuradiyya tare da bude fili don amfanin kasar nan

FCT, Abuja - Bishop Matthew Kukah, limamin Katolika na Sokoto Diocese, ya ce zaben 2023 zai bai wa ‘yan Najeriya wata dama na gyara kuskuren da suka yi.

Malamin ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli a Abuja a wani taron da cibiyar Kukah Center and Open Society Initiative For West Africa (OSIWA) suka shirya.

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah
Kukah ya ce Najeriya na bukatar shugabanni masu mutunci Hoto: The Kukah Centre
Asali: Facebook

Bishop din ya koka kan cewa matasan Najeriya na ganin ba su da karfi kwata-kwata saboda kasar na kan turba mai hadari, jaridar This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya caccaki mulkin APC, ya ce za ta ruguza Najeriya kafin 2023

A cewarsa, ‘yan Najeriya sun tsici kansu a kasar da ke cinye ‘ya’yanta.

Ya ce:

“Wannan hanya ce mai hatsari da muke bi. Matasanmu suna jin gazawa. Mun hadu da kasar da ke cinye ‘ya’yanta, muna fuskantar makoma na rashin tabbas a nan gaba. Ba shi yiwuwa, hatta babbar makiyar Najeriya ba za ta taba tunanin cewa a nan za mu kasance ba.”

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Kukah ya kuma bayyana cewa dimokiradiyya da mulkin kama karya ba za su iya zama tare ba.

Bishop din ya ce kungiyoyin farar hula sun ba da gudummawa ga halin da kasar ke ciki a yanzu.

Ya bayyana cewa da halin da kasar ke ciki yanzu bai tabarbare ba idan da jama’a ba su kwanta da wuri ba bayan kasar ta koma ga mulkin farar hula.

Bishop Kuka yayi kira ga shugabannin Najeriya da su daina daukar rantsuwar da basu kiyayewa

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

A gefe guda, Mathew Hassan Kuka, babban limamim cocin katolika na jihar sokoto, ya jajanta yadda shugabannin siyasa ke rantsuwa da kuma yadda rashin tsaro ke hauhawa a kasar nan.

Ya bukaci 'yan siyasa da su daina daukan rantsuwar da ba zasu iya cikawa ba, HumAngle ta ruwaito.

Bishop Kuka ya sanar da hakan ne a Kaduna, ranar Talata, 1 ga watan Yunin 2021 yayin bikin birne marigayi Rabaren Alphonsus Yashim Bello, limamin cocin katolika na Katsina wanda 'yan ta'adda suka kashe a ranar Juma'a, 21 ga watan Mayun 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng