Ofishin binciken hatsari ya yi martani ga rade-radin hatsarin jirgin sama a filin jirgin Ilorin

Ofishin binciken hatsari ya yi martani ga rade-radin hatsarin jirgin sama a filin jirgin Ilorin

  • Ofishin binciken hatsari ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar kin binciko lamarin da ke kewaye da fashewar taya a Filin jirgin saman Ilorin
  • Wani mai magana da yawun ofishin ya karyata rahotannin da ke nuna cewa wani mummunan hatsari ya faru a filin jirgin
  • Har yanzu Hukumar Filin Jirgin Sama ta Najeriya ba ta fitar da wani bayani a hukumance game da lamarin ba

Ofishin Binciken Hadari (AIB) ya yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa wani jirgin sama na daya daga cikin manyan kamfanonin jiragen saman kasar ya fadi a kan titin jirgi a filin jirgin saman Ilorin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tayoyin jirgin sun tarwatse bayan ya sauka a filin jirgin saman Ilorin na jihar Kwara a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli.

Ofishin binciken hatsari ya yi martani ga rade-radin hatsarin jirgin sama a filin jirgin Ilorin
AIB ya ce babu wani hatsarin jirgin sama da ya faru a filin jirgin kasar Hoto: Murtala Muhammed International Airport - Lagos Airport - Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar ta ce lamarin ya faru ne lokacin da jirgin ke rangaji zuwa wajen sauka a filin jirgin.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Sojoji Sun Fatattaki Mayaƙan Boko Haram Daga Wani Gari a Yobe

Sai dai, mai magana da yawun kamfanin jirgin, Stanley Olise, ya shaida wa jaridar cewa an gyara tayar sannan kuma aka dauke jirgin daga filin tashin.

Har ila yau da yake tabbatar da faruwar lamarin, Ofishin Binciken Hatsari, hukumar bincike da ke kula da dukkan hadurra da abubuwan da suka shafi jirgin sama a Najeriya, ta ce babu wani hatsarin jirgin sama.

AIB ya tabbatar da fashewar taya a yayin sauka

Mai magana da yawun kungiyar ta AIB, Tunji Oketumbi, ya bayyana cewa tayar jirgin ya fashe a yayin sauka.

Ya ce:

‘’Eh. Ya faru jiya. Masu bincike na AIB sun auna lamarin kuma sun yanke shawarar ƙin yin bincike. An saki jirgin ga matukin.
"Jinkirin da FAAN (Hukumar filayen jiragen saman Najeriya) da Airpeace suka yi wajen bude filin jirgin ya kasane saboda farfadowar jirgin sama daga wajen tashi."

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai wankin mota ya fada cikin matsala bayan ya tuka motar da aka kawo masa wanki zuwa wajen siyan teba da miya sannan ya yi kaca-kaca da motar.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

A cikin bidiyon da @drive234 ya wallafa a TikTok, an ga mai wankin motar yana duke kan gwiwowinsa tare da rokon mai motar da ya gafarta masa.

Motar ta lalace sosai kuma saurayin ya yi nadama amma bidiyon bai nuno ko an yafe masa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng