Mai wankin mota ya ragargaza Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci

Mai wankin mota ya ragargaza Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci

  • Wani matashi dan Najeriya ya fada cikin matsala bayan ya tuka motar da aka bashi wanki zuwa wajen siyan teba da miya
  • Mutumin da ba a san kowanene ba ya buga motar kirar Mercedes-Benz GLC kuma ya yi raga-raga da ita; ana iya ganin sa a bidiyo kan gwiwowinsa tare da rokon mai shi
  • ‘Yan Najeriya sun mamaye shashin sharhi don bayyana ra’ayinsu bayan an wallafa shi kan TikTok da Instagram

Wani dan Najeriya mai wankin mota ya fada cikin matsala bayan ya tuka motar da aka kawo masa wanki zuwa wajen siyan teba da miya sannan ya yi kaca-kaca da motar.

A cikin bidiyon da @drive234 ya wallafa a TikTok, an ga mai wankin motar yana duke kan gwiwowinsa tare da rokon mai motar da ya gafarta masa.

Kara karanta wannan

An Rasa Ran Mutum 1 a Farmakin da ‘Yan Bindiga Suka kai Maitama Dake Abuja

Mai wankin mota ya ragargaza mota kirar Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci
An gano mutumin yana rokon gafara Hoto: @drive234/TikTok
Asali: UGC

Motar ta lalace sosai kuma saurayin ya yi nadama amma bidiyon bai nuno ko an yafe masa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake wallafa bidiyon a Instagram, wani shahararren dan Najeriya kuma mai tasiri a kafofin sadarwa Tunde Ednut ya rubuta cewa:

"Me ya sa ka tuka motar wani da ke hannunka? Mai wankin mota ya dauki motar abokin harka ya je ya sayi Eba, Ewedu, 2 Kpomo da naman shanu 1. Dubi abin da ya yi wa motar wani a yanzu."

Mutane da dama sun yi sharhi ga rubutun Tunde Ednut

@gifty_suzanne ya ce:

“Idan yan kauyenku suka kasance a kan lamarinka.”

@chocolatesandra_ yayi tsokaci:

"Wannan rayuwar ta karya ba za ta jefa mu cikin matsala ba."

@akeula_trendy ya ce:

"Lmao, jin daɗin minti 30, ɗaurin shekaru 30."

A wani labarin, rundunar sojojin saman Nigeria, NAF, a ranar Alhamis ta karbi rukuni na farko na jiragen sama na yaki kirar A-29 Super Tucano daga kasar Amurka, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ɗan Najeriya Na Shirin Wuf da Wata Baturiya Da Suka Hadu A TikTok

Edward Gabkwet, direktan sashin hulda da jama'a da watsa labarai na hedkwatar rundunar sojojin saman Nigeria da ke Abuja ne ya sanar da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel