Cikakken Bayani: Sojoji Sun Fatattaki Mayaƙan Boko Haram Daga Wani Gari a Yobe

Cikakken Bayani: Sojoji Sun Fatattaki Mayaƙan Boko Haram Daga Wani Gari a Yobe

  • Sojojin Nigeria sun fatattaki mayakan kungiyar Boko Haram da suka yi niyyar kai hari Geidam a Yobe
  • Wani mazaunin garin Geidam, Modu Ali, ya tabbatar da lamarin yana mai cewa sojojin sun samu bayanin zuwan yan ta'addan
  • Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya jinjinawa jarumtar sojojin yayin mika godiyarsa ga jami'an tsaron bisa dakile harin

Jami'an tsaro sun dakile wani gari da aka yi niyyar kaiwa a garin Geidam a jihar Yobe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mayakan Boko, wanda suka kai mummunan hari a Geidam watanni da suka gabata sun sake yunkurin kai hari a gari a yammacin ranar Laraba.

Cikakken Bayani: Sojoji Sun Fatattaki Mayaƙan Boko Haram Daga Wani Gari a Yobe
Dakarun sojojin Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

Amma dakarun sojojin sun yi galaba a kansu sun tilasta su tserewa.

Modu Ali, wani mazaunin garin na Geidam ya ce an tsegunta wa jami'an tsaron cewa yan ta'addan za su kawo harin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna garin da suka tsere daga Geidam bayan garin bayan harin da aka kai a baya su dawo domin yin shagulgulan sallah.

Gwamna Mai Mala Buni ya jinjinawa sojoji

Da ya ke martani kan lamarin, Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya jinjinawa jami'an tsaron bisa jarumtarsu.

A sanarwar da gwamnan ya fitar ta bakin hadiminsa Mamman Mohammed, Buni ya ce:

"Abin farin ciki ne ganin cewa duk da makiya sun tsere, sojojin sun bi sahunsu sun kawar da wadanda suka shirya kai musu harin kwantar bauna.
"Gwamnatin Yobe da jama'ar jihar suna godiya bisa wannan jarumta da tsare gari da ya bawa mutanen Geidam damar ci gaba da shagulgulan sallah cikin zaman lafiya."

Ya yi bayanin cewa daukan mataki kafin abu ya faru zai magance hare-hare da rasa rayyukan mutane.

Gwamnan ya yi kira ga al'umma su rika taimakawa jami'an tsaro da bayannai masu amfani kuma a kan lokaci don hakan zai taimaka wurin dakile hari.

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

A wani labarin daban, babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.

Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel