Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

  • Gwamnan jihar Borno ya tallafawa wasu sojojin da suka ji rauni a kokarin fatattakar 'yan ta'adda a jihar
  • Ya sanar da bayar da tallafin ne yayin wata liyafar cin abinci da aka shirya a wani yankin jihar ta Borno
  • Rahoto ya bayyana adadin makudan miliyoyin da gwamnan ya sanar domin ba jatruman sojojin

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10 a jiya Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

KARANTA WANNAN: Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Gwamna Zulum ya yi wa sojojin Najeriya goma ta arziki gabanin sallah
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum | Hoto: solacebase.com
Asali: UGC

Manjo Janar Farouq Yahaya ya yaba wa gwamnan kan taimakon da yake bai wa dakarun rundunar sojin Najeriya.

Ya ce an haDa liyafar cin abincin sallar ne Karfafa gwiwar dakarun da ke fagen daga.

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Babban hafsan sojoji, Janar Faruk Yahaya, ya baiwa 'yan Najeriya tabbacin cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da mai da hankali wajen magance dumbin matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Yahaya ya bayar da tabbacin ne a sakonsa na fatan alheri ga hafsoshi, sojoji da danginsu kan bikin Babbar Sallah na 2021, ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, a Abuja.

Ya ce bikin na Babbar Sallah ya nuna kyawawan dabi'u na biyayya, mika kai da sadaukarwa wadanda su ne manyan kwarewa ta aikin sojoji, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Boko Haram: An baiwa dakarun sojin Najeriya sabon umarni kan yakar ta'addanci

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

A wani labarin, Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba Naira miliyan 21.7 ga gundumomi 87 don sayan shanun sallah ga marayu, Daily Trust ta ruwaito.

An ba kowace daga cikin gundumomin N200,000 na sayen saniya da kuma N20,000 don jigilar ta.

A yayin kaddamar da bayarwar, Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar Said, ya gode wa gwamnatin jihar bisa ci gaba da wannan aikin duk da raguwar albarkatun ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.