Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno

Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno

  • Farfesa Zulum na jihar Borno ya jaddada cewa shi ke jagorancin jihar Borno
  • Gwamnan ya musanta rade-radin dake yawo na cewa Boko Haram ta nada sabon gwamna
  • A kafafen sada zumunta ake bayyana wani Abba Kaka a matsayin gwamnan da miyagun suka nada

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya musanta rahoton dake yawo na nada gwamna a wasu yankunan jihar Borno da Boko Haram tare da ISWAP suka yi.

A makon da ya gabata, bidiyon da ake zargin na nada gwamnan Boko Haram a Borno ne ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar rikon kwarya ta 'yan ta'addan ta samu shugabancin wani Abba Kaka, wanda aka nada a matsayin shugaban wasu yankunan Borno.

KU KARANTA: Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu

Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno
Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: APC ta rushe kwamitin rikon kwaryan jam'iyyarta na jihar Zamfara

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana matakansa da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Amma yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, gwamnan ya karyata wannan labarin, Daily Trust ta wallafa.

Ya jaddada cewa "shi ke jagorantar jiharsa."

Zulum yace mulkinsa baya bincikar al'amarin

"Har yanzu bamu fara bincikar sahihancin rahoton nada gwamnan Borno da 'yan ta'adda suka yi ba. A matsayina na gwamnan jihar, a tunani na bai dace in yi magana kan abinda bani da iliminsa ba cikakke."

Rahoton bashi da sahihanci, a kafar sada zumunta yake

A yayin da aka tambaya gwamnan ko zai yi bincike, Gwamna Zulum yace a'a, ya dora laifin rahoton ga kafafen sada zumunta.

Ya kara da cewa: "Ba zan yi bincike ba saboda rahoton bashi da sahihanci. Rubutu ne kawai kuka gani a Facebook. Ku 'yan jarida ne, ina tunanin sai mun san ingancin rahoto kafin mu yi tsokaci a kai.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

"Ni dai abinda na sani shine, ni ne gwamnan jihar Borno kuma bani da wani labari na cewa akwai wata gwamnati ta daban. Tabbas ni ke shugabantar jihar."

A wani labari na daban, diyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua da mijin tsohuwar matar gwamnan Taraba, Hauwa Suntai suna shari'a kan wani fili dake yankin Kado a babban birnin tarayya na Abuja.

PRNigeria ta tattaro cewa Zainab Yar'Adua tsohuwar matar tsohon gwamnan Kebbi, Saidu Dakingari, ta bayyana cewa fili mai adireshi 506, Cadastral Zone B09, yankin Kado a babban birnin tarayya Abuja.

Duk da kamfaninta mai suna Marumza Estate Development Company Limited, Yar'Adua ta maka wani kamfani mai suna Itban Global Resources Limited da kuma shugabanshi, Halliru Saad Malami a gaban kotu tare da ministan Abuja kan rikicin filin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: