Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu

Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Kabara uwa hedkwatarta
  • An gano cewa a a gurfanar da malamin a gaban kotu bayan mukabalar da aka yi dashi ranar Asabar
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta ce gayyatar da tayi masa bata dawata alaka da mukabalar da aka yi

Kano

Mukabalar da aka dade ana jira tsakanin Sheikh Abduljabbar da sauran malaman Kano ta kare da rigima domin an kasa tsayawa a tsayayyar matsaya.

Bayan kammala mukabalar, Daily Trust ta gano cewa an shirya mika malamin gaban kotu kan laifukan batanci. 'Yan sanda sun mika takarda domin ya bayyana a gaban hedkwatar 'yan sanda a ranar Litinin.

KU KARANTA: Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira

Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu
Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan gwamnan Ogun yana gyara cunkoson titi da dare sun janyo cece-kuce

Wata majiya makusanciya da malamin ta sanar da Daily Trust cewa tuni dama an shirya wadannan zargin kan Abduljabbar wanda aka shirya dauka daga wurin mukabalar wacce aka yi a hukumar Shari'a ta jihar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13

'Yan sandan Kano sun magantu

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, DSP Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da gayyatar da 'yan sanda suka kaiwa Abduljabbar a daren jiya amma ya tabbatar da cewa bata da alaka da mukabalar ranar Asabar.

"Yana daga cikin tuhumarsa da ake yi tunda dama belinsa aka yi. Akwai wani korafi da wasu malamai suka kaiwa 'yan sanda wanda suke aiki a kai kuma yana zuwa domin bincike.

"Ya dace ya zo ranar Juma'a amma saboda shirin mukabalar, an dage ranar domin barinsa ya shirya da kyau," Kiyawa yace.

A wani labari na daban, Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa ta yi wallafa kan APC a watan Augustan 2020 akasin yadda ta yi ikirari a ranar Alhamis yayin da ta bayyana a gaban majalisar dattawa.

A yayin da ta bayyana gaban kwamitin hukumar zabe na majalisar dattawa, Onochie ta yi ikirarin cewa ta bar siyasar bangaranci bayan an sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.

Kara karanta wannan

Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri

Hadimar Buharin a fannin yada labarai ta je tantancewa ne a matsayin kwamishinan INEC daga jihar Delta bayan zabenta da shugaba Buhari yayi a watan Oktoban da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel