Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

  • Bayan komawar gwamnonin PDP biyu zuwa jam'iyyar APC mai ci a Najeriya, shugaban Buhari ya karbi bakwancinsu
  • Ya karbe su ne a fadarsa dake Aso Rock a babban birnin tarayya Abuja tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar ta APC
  • Babu dai wani bayani da ya bayyana cewa ga abinda aka tattauna yayin ganawar wacce aka yi ranar Litinin 12 ga watan Yuli

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya karbi bakuncin gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da takwaransa na jihar Kuros Riba, Ben Ayade, a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin.

Kwanan nan duka gwamnonin biyu suka fice daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

KARANTA WANNAN: ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

Ko da yake har yanzu ba a san cikakken bayani game da ganawar tasu ba, amma, an watsa hotuna a shafin Facebook na Gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kotu ta sanar da ranan sauraran karar da PDP ta shigar kan sauya shekar gwamna Matwalle

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC
Shugaba Muhammadu Buhari | Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC
Shugaba Buhari da Gwamna Ayade | Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

dauke da hotunan, an rubuta:

“Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sababbin Gwamnonin APC na Kuros Riba da na jihar Zamfara karkashin jagorancin Shugaban Rikon kwarya na APC a Fadar Shugaban Kasa, Abuja | 12 gatafe... Yuli 2021."

Rikici: Mataimakin gwamna na kokarin karbe kujerar Matawalle, PDP ta yi martani

An rahoto cewa Mahdi Aliyu Gusau, mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya samu goyon bayan jam’iyyar PDP don karbar kujerar Bello Matawalle a matsayin gwamnan jihar dake a arewa maso yamma.

Wannan ya biyo bayan sauya shekar da Gwamna Matawalle ya yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki tare da sauran zababbun masu rike da mukaman siyasa a jihar.

Sai dai, Gusau ya tsaya, yana mai cewa ba a zabe shi don ya fice daga PDP zuwa wata jam'iyyar ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

Mataimakin gwamnan ya yi hasashen matakin da zai dauka na tsige Matawalle a kan hukuncin Kotun Koli na 2019 wanda ya soke nasarar da dukkan ‘yan takarar APC suka yi a zaben.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: PDP ta je kotu, ta nemi a kwace kujerar gwamna Matawalle da mataimakinsa

Amma, an tattara cewa, rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara na toshe yunkurin Gusau na karbar mukaminsa na gwamna, lamarin da ya haifar da martani daga PDP a ranar Lahadi, 11 ga watan Yuli.

KARANTA WANNAN: Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

PDP ta je kotu, ta nemi a kwace kujerar gwamna Matawalle da mataimakinsa

A wani labarin, Jam’iyyar PDP ta nemi wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta kori Gwamnan Zamfara da Mataimakinsa - Bello Muhammad Matawalle da Mahdi Aliyu Gusau - kan ficewarsu daga Jam’iyyar zuwa Jam’iyyar APC, The Nation ta ruwaito.

Bukatar tana daga cikin abinda PDP ta nema a wata kara mai lamba: FHC / ABJ / CS / 489/2021 da aka gabatar da sunayen mambobin PDP biyu daga jihar Zamfara - Sani Kaura Ahmed da Abubakar Muhammed.

Masu shigar da karar suna kalubalantar cewa, saboda hukuncin da Kotun Koli ta yanke a baya, kan cewa APC ba ta da wani dan takara a zaben gwamna a 2019 a Jihar Zamfara, ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel