Gwamnan Gombe ya bayyana matakan da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu
- Gwamnan jihar Gombe ya bayyana matakin da ya dauka don tabbatar da zaman lafiya a jiharsa
- Ya bayyana cewa, jihar ta Gombe ta zama ita ce dama-dama idan aka kwatanta da sauran jihohi
- Ya bayyana haka ne yayin da yake bayyana matakin gina manyan makarantu kusa da jami'an tsaro a jihar
Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa na gina manyan makarantu kusa da hukumomin tsaro don kare dalibai a duk lokacin da suka fuskanci barazanar sata daga 'yan bindiga.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai na Fadar Gwamnatin Trayya a Abuja bayan ganawa da Shugaban Ma’aikata na Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi
A cewarsa:
“Mun yi gwajin yanayin rauni ga dukkan makarantu kuma mun sanya jami’an tsaro na cikin gida; 'yan banga, su yi aiki tare da jami'an tsaro na musamman domin kiyaye makarantunmu daga hare-hare.
“Sama da haka, abinda muka yi don inganta tsaro ya yi tasiri a cikin makarantu kuma mun tattara kokarinmu wajen gina manyan makarantu wadanda za su kunshi dimbin adadi don rage damar sata.
A cewar gwamnan, gina manyan makarantu zai taimaka ta yadda:
"Duk inda dalibai suka gamu da irin wannan hadarin, mun kawo su kusa zuwa ga manyan hukumomin tsaro domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
“Hakan ya yi nasarar kawo zaman lafiya a makarantun mu. Don haka, makarantu da sauran al’umma suna zaune lafiya a Gombe kuma muna gode wa Allah a kan hakan."
Gombe ta taba fuskantar rikicin makiyaya da manoma
Ya ce saboda Gombe ta raba iyaka da wasu jihohin arewa maso gabas biyar, rikicin makiyaya da manoma ya haifar da rashin tsaro a Gombe a baya.
Nigerian Tribune ta ruwaito lokacin da yake bayyana ci gaban da aka samu jihar, Yahaya ya ce:
“Amma mun kasance masu himma kuma muna bin diddigin cibiyoyin da abun ya shafa kowace rana, misali, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da hukumomin tsaro, suna kokarin gina fahimtar juna da kyakkyawar alaka tsakanin mutanenmu.
“Zan iya cewa, idan aka kwatanta da saura, Gombe tana da kwanciyar hankali kuma muna gode wa Allah a kan haka; muna matukar godiya da hadin kai da fahimtar mutanenmu. "
KARANTA WANNAN: Kotu ta sanar da ranan sauraran karar da PDP ta shigar kan sauya shekar gwamna Matwalle
Kaduna: Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga
A wani labarin, Sojoji sun mamaye dajin Kaduna don neman Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu da wasu danginsa 10 da aka yi garkuwa da su a karshen mako, The Nation ta ruwaito.
Satar sarki ya biyo bayan sace wasu dalibai da aka yi a wata makaranta duk dai a jihar ta Kaduna, lamarin da ya sake jefa al'umma cikin tsoro.
Jami'an tsaro na aiki don ganin an ceto su. Baya ga sojojin da ke gandun daji, rundunar 'yan sanda ta ce suna sa ran rundunar dabaru ta Babban Sufeto-Janar na 'Yan Sanda zata ba su goyon baya ta fasaha.
Asali: Legit.ng