APC ta rushe kwamitin rikon kwaryan jam'iyyarta na jihar Zamfara

APC ta rushe kwamitin rikon kwaryan jam'iyyarta na jihar Zamfara

  • Kwamitin rikon kwarya na APC na kasa ya rushe kwamitin shugabanci na jam'iyyar a Zamfara
  • A take kwamitin ya sake nada sabon shugaba, mataimaki da sakataren jam'iyyar a jihar
  • Hakan ya biyo baya ne sakamakon sauya shekar da gwamna Matawalle yayi a jihar zuwa APC

APC, Zamfara

Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na kasa, ya rushe kwamitin shugabannin jam'iyyar na jihar Zamfara.

Sanata John Akpanuodedehe, sakataren CECPC na kasa, ya sanar da rushewar a wata wasika mai kwanan wata 9 ga Yulin 2021 kuma aka aikata ga shugaban kwamitin rikon kwaryan da aka rushe, Lawal Liman.

KU KARANTA: Hotunan gwamnan Ogun yana gyara cunkoson titi da dare sun janyo cece-kuce

APC ta rushe kwamitin rikon kwaryan jam'iyyarta na jihar Zamfara
APC ta rushe kwamitin rikon kwaryan jam'iyyarta na jihar Zamfara. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kwafin wasikar wacce aka baiwa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadi a garin Gusau, ta ce an rushe kwamitin a take ne.

"Na rubuto in sanar da ku cigaban da aka samu a cikin jam'iyyarmu a jihar. Kwamitin rikon kwarya na kasa ya amince da rushe dukkan shugabanni jam'iyyar a matakin gunduma, karamar hukuma da jiha baki daya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna

“Wannan cigaban zai fara aiki ne a take," wasikar tace.

Ta kara da bayyana cewa an kafa kwamitin rikon kwarya na mutum uku wanda zai kula da al'amuran jam'iyyar a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sabon kwamitin rikon kwaryan ya hada da Hassan Mohammed a matsayin shugaban kwamitin, tsohon mataimakin shugaban kwamiti shine Muntari Anka da Abdullahi Shinkafi a matsayin sakataren jam'iyyar na jihar.

Kwamitin kasa na rikon kwaryan ya mika godiyarsa ga tsoffin shugabanni kuma yayi kira garesu da su bada goyon bayan da sabbin shugabannin na jihar ke bukata.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa wannan canjin shugabannin jam'iyyar ya biyo bayan sauya shekar da Gwamna Bello Matawalle na jihar yayi.

Aranar 29 ga watan Yuni ne takwaran Gwamna Matawalle na jihar Yobe ya karba Matawalle zuwa jam'iyyar APC, The Guardian ta ruwaito.

An bayyana Matawalle a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar Zamfara kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex, ya mutu

KU KARANTA: An bankado: Duk da tace ta bar siyasa, Onochie ta yi wa APC wallafa a 2020

A wani labari na daban, wani tsoho mai shekaru 90 mai suna Yusuf Yarkadir ga shiga hannun hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) a kan siyar da kwayoyi ga matasa a kauyensu mai suna Yarkadir a karamar hukumar Rimi ta jihar.

Yayin da aka tuhume shi, tsohon ya sanar da cewa shi ke siyarwa matasan yankin wiwi na tsawon shekaru takwas, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya sanar, duk da wanda ake zargin ya kasa bayyana inda yake samun kayansa, ya sha alwashin barin irin harkar duk da ya so hakan a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng