Rikici ya barke tsakanin iyalin Yar'adua da Mijin tsohuwar matar Danbaba Suntai

Rikici ya barke tsakanin iyalin Yar'adua da Mijin tsohuwar matar Danbaba Suntai

  • Rikici ya rincabe tsakanin Zainab Yar'Adua da mijin tsohuwar matar gwamnan Taraba, Hauwa Suntai
  • An gano cewa wani fili ne ya hada rigimar wanda Zainab Yar'Adua ke ikirarin mallakinta ne kuma Halliru Saad Malami shima haka
  • Zainab ta ce ta mallaki filin ne sakamakon kyautar da FCDA ta bata bayan ta siya filin daga hannun wani kamfani mai suna Itban

Diyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua da mijin tsohuwar matar gwamnan Taraba, Hauwa Suntai suna shari'a kan wani fili dake yankin Kado a babban birnin tarayya na Abuja.

PRNigeria ta tattaro cewa Zainab Yar'Adua tsohuwar matar tsohon gwamnan Kebbi, Saidu Dakingari, ta bayyana cewa fili mai adireshi 506, Cadastral Zone B09, yankin Kado a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: A karon farko, an gano mugun irin Covid-19, SARS-Cov-2 a Najeriya

Rikici ya barke tsakanin iyalin Yar'adua da na Danbaba Suntai
Rikici ya barke tsakanin iyalin Yar'adua da na Danbaba Suntai. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: An bankado: Duk da tace ta bar siyasa, Onochie ta yi wa APC wallafa a 2020

Kara karanta wannan

El-Rufai ya bada hutun kwana ɗaya a Kaduna domin zaman makokin Bantex

Duk da kamfaninta mai suna Marumza Estate Development Company Limited, Yar'Adua ta maka wani kamfani mai suna Itban Global Resources Limited da kuma shugabanshi, Halliru Saad Malami a gaban kotu tare da ministan Abuja kan rikicin filin.

Malami wanda dan uwa ne ga Turai Yar'Adua shine mijin Hauwa Suntai, tsohuwar matar marigayin tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai, Daily Nigerian ta ruwaito.

Suntai wanda hatsarin jirgin sama ya ritsa da shi a watan Oktoban 2012 kuma ya mutu a ranar 28 Yunin 2017, a Houston dake Florida a Amurka.

Duk da lauyanta, Sebastine Hon SAN, ya shigar da kara da bukatar wata babbar kotu dake Abuja da ta bada umarnin tsayar da wacce ake kara da ta daina amfani da filin da ake fada kan shi.

Ta yi ikirarin cewa ta samu filin ne sakamakon kyautar da aka bata ta hannun FCDA daga Itban Global Resources Limited wanda aka siya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna

Amma kuma a wata takarda da ta ci karo da ikirarin, Malami da kamfaninsa suka fitar ta hannun lauyansu Remi Olatubora SAN, sun zargi Yar'Adua da amfani da wani Sani Rabo da wasu wurin samun takradun bogi domin mallake filin.

Itban ya zargi wani Sani Rabo wanda ya san tarihin filin da hada baki da wasu wurin fitar da takardun bogi, karfin ikon antoni da sauran hanyoyin damfara wurin mallakar filin.

A wani labari na daban, wani tsoho mai shekaru 90 mai suna Yusuf Yarkadir ga shiga hannun hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) a kan siyar da kwayoyi ga matasa a kauyensu mai suna Yarkadir a karamar hukumar Rimi ta jihar.

Yayin da aka tuhume shi, tsohon ya sanar da cewa shi ke siyarwa matasan yankin wiwi na tsawon shekaru takwas, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya sanar, duk da wanda ake zargin ya kasa bayyana inda yake samun kayansa, ya sha alwashin barin irin harkar duk da ya so hakan a baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex, ya mutu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel