'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyu da wasu matan aure biyu a jihar Niger

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyu da wasu matan aure biyu a jihar Niger

  • Yan bindiga sun halaka wasu jami'an yan sanda biyu da wasu mata biyu a jihar Niger
  • Yan bindigan da sun kashe yan sandan ne a Kompani Bobi bayan sun kai hari wasu kauyuka
  • Matan biyu su kuma sun rasu ne sakamakon harbe-harben yan bindigan a lokacin da suke tserewa

Wasu yan bindiga sun kashe jami'an yan sanda biyu da wasu mutanen biyu a Kamponi Bobi, karamar hukumar Mariga da ke jihar Niger, Daily Trust ta ruwaito.

Hare-haren da aka kai a daren ranar Alhamis da safiyar Juma'a ya yi sanadin jikkatan wasu mutanen masu yawa.

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyu da wasu matan aure biyu a jihar Niger
Taswirar Jihar Niger. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Gwamnatin Katsina za ta wajabtawa kowanne baligi harajin N2000, shanu kuma N500 matsayin Jangali

An gano cewa yan bindigan sun fara kai hari ne kauyen Makura misalin karfe 10 na dare a ranar Alhamis sannan suka ziyarci wasu garuruwan uku kafin safiyar ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari

Daily Trust ta tattaro cewa yan bindigan, bayan kai harin a garuruwan tare da sace shanu, sun tafi wani wurin da ake gini a Kompani Bobi inda suka kaiwa yan sandan da ke wurin hari suka kashe biyu.

Ganin cewa safiya ta fara yi, yan bindigan suka fara harbe-harbe domin firgita mutane a hakan ne suka kashe wasu mata biyu tare da raunta mutane da dama.

Matan biyu dukkansu matan wani mutum ne da ke tafiya da iyalansa zuwa Kontagora amma harin ya ritsa da su.

KU KARANTA: Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

Majiyar ta ce:

"Duk da cewa shi mutumin bai samu rauni ba, watakila domin shine ya ke tuki, biyu daga cikin matansa sun rasu sakamakon harbin bindigan yayin da daya tana asibiti tana jinya."

Ba a samu halin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ba a lokacin hada wannan rahoton domin wayansa baya shiga.

Kara karanta wannan

Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma

'Yan bindiga sun kashe mutum 19 a Katsina, sun ƙona gidaje sun sace dabbobi masu yawa

A wani rahoton, a kalla mutane 19 ne suka mutu sannan wasu dama an neme su an rasa bayan yan bindiga kan babura sun kai hari kauyen Tsauwa a karo na biyu a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina a yammacin ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani majiya daga kauyen ya ce maharan sun afka garin ne misalin karfe 5.45 na yamma.

Yan bindigan sun tarwatsa mazauna kauyen suka rika binsu a kan babura, suka harbe 19 har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel