Gwamnatin Katsina za ta wajabtawa kowanne baligi harajin N2000, shanu kuma N500 matsayin Jangali
- Gwamnatin jihar Katsina zata gabatar da tsarin biyan harajin N500 akan kowacce saniya ga makiyayan da suke jihar
- Kwamishinan kasafi da tattalin jihar, Alhaji Faruk Jobe ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan kammala wani taro
- Ya kara da bayyana dawowa da tsarin biyan kudin cigaba N2000 ga kowanne baligi mazaunin jihar wanda a cewarsa dama akwai tsarin
Gwamnatin jihar Katsina za ta fara karbar harajin Jangali na N500 akan kowacce saniya da ke jihar duk shekara kamar yadda News Wire ta ruwaito.
The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta gabatar da tsarin amsar kudin bunkasa jihar da kuma jangalin shanu.
Alhaji Faruk Jobe, kwamishinan kasafi da tattalin jihar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan wani taro na masu ruwa da tsakin jihar wanda gwamna Aminu Masari ya shirya.
DUBA WANNAN: An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel
Jobe ya ce kwamitin ta shirya tsarin bin lungu da sako don amso harajin a fadin jihar.
“Bayan isowar wannan rahoton ne muka gane cewa duk wani baligi da ke zaune a jihar, mace ko namiji zai dinga biyan N2000 a matsayin harajin raya jiha da cigaba a kowacce shekara.
“Batun harajin shanun, ‘Jangali,’ duk wani mai saniya zai dinga biyan N500 kowacce shekara, kuma zamu gabatar da wannan batun ga majalisar jihar don tabbatar da tsarin,” a cewarsa.
Da aka tambayeshi idan kudin ba zai rubanya ga ma’aikatan gwamnati ba baya ga wanda ake zaftarewa a albashinsu, kwamishinan ya ce nasu harajin ya danganta da yawan albashinsu ne.
A cewarsa, wannan tsarin da gwamnatin jihar ta shirya sunanshi “kudin cigaba”, don haka akwai bambanci da haraji’.
An yi wa matan aure marasa aikin yi rangwame
Ya kara da cewa matan auren da basa aiki bazasu biya ko sisi ba amma duk wata mata da take aiki sai ta biya.
KU KARANTA: Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO ba
A cewar kwamishinan, dama akwai wannan tsari tuntuni, amma siyasa ta rusa shi a 1979.
“Yanzu kuma mun kara dawo dashi.”
“Kafin mu fara gwamnati zata tabbatar anyi kidayar duk wasu baligai da suke jihar don asan yawan jama’an da zasu biya da kuma wadanda bazasu biya ba.
“Wannan tsarin ne zai bayyana mana ayyukan jama’a da sauran bayanai na musamman don sanin yadda zamu bullo wa lamarin,” a cewarsa.
A cewar Jobe irin tsarinnan za ayi akan shanu don asan yawansu da kuma kudaden da za a samu a fadin jihar.
Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara
A wani labarin daban, wata babban kotun jihar Kano, a ranar Talata ta ci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tarar N800,000 bayan ya janye karar bata suna da ya shigar kan mawallafin jaridar intanet ta Daily Nigerian, Daily Trust ta ruwaito.
Ganduje ya maka mawallafin Ja'afar Ja'afar a kotu be saboda labari da bidiyon da ya wallafa inda aka gano wani da aka shine ke saka kudaden kasashen waje a cikin aljihunsa.
Kotun, karkashin jagorancin Mai shari'a Suleiman Danmallan, wadda ta amince da dakatar da shari'ar, ta umurci gwamnan ya biya Ja'afar Ja'afar da kamfaninsa na jaridar N400,000 kowannensu.
Asali: Legit.ng