Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma

Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma

  • Karuwar tashe-tashen hankula ka iya dankwafar da dimokoradiyyar Najeriya a 2023, a cewar Ingila
  • Sannan Ingilar ta bukaci sauye-sauye a rundunonin soja da ‘yan sanda cikin gaggawa
  • Tsohon Shugaban Kasar mulkin sojan ya ce sauya shekar da ‘yan siyasar ke yawan yi mummunan abu ne

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janal Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), a jiya Alhamis ya yi gargadi game da yawaitar sauya sheka da ‘yan siyasa ke yi, yana mai cewa hakan zai haifar da rudani da rigingimun da za su kara haifar da zullumi a kasa.

Tsohon Shugaban, a yayin kaddamar da shirin samar da zaman lafiya da hadin kan tsaro da gwamnonin jihohi 36 suka yi jiya a Abuja, ya yi gargadi kan yawaitar sauya sheka da ‘yan siyasa ke yi daga wata jam’iyyar siyasa zuwa wata.

Yana tsokaci ne game da yadda 'yan siyasa suka sake lale a tafiyar siyasarsu gabanin babban zaben 2023; inda wadansu daga cikinsu, musamman gwamnoni da ‘yan majalisa suke canza jam'iyya, rahoton Thisday.

Kara karanta wannan

Wani babban Jigon PDP Ya Bi Sahun Gwamnoni da Yan Majalisu, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Akalla gwamnoni uku ne suka sauya sheka daga Jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki tun a watan Nuwambar bara lokacin da gwamnan Jihar Ebonyi, Cif Dave Umahi, ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma APC.

Sauran wadanda suka sauya sheka sun hada da Gwamnonin jihohin Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade da na Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle.

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Janar Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma
Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma Hoto: Press Conference

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Idan ba'a shawo kan matsaloli ba Najeriya na iya hargitsewa nan da 2023

Har ila yau, a wajen taron, Ofishin Jakadancin Burtaniya a Najeriya, ya yi gargadin cewa rikicin da ke fuskantar Najeriya, idan ba a hanzarta magance shi ba zai iya hargitsa tsarin dimokoradiyyar kasar da ma babban zaben 2023, riwayar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita

Har ila yau, ofishin ya bukaci da a yi garambawul cikin gaggawa a rundunonin soja da na ‘yan sandan Najeriya, yana mai jaddada cewa amfani da karfin soja da ‘yan sanda kadai ba zai zama mafita wajen magance kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya.

A cewar jakadan hanyar da za a bi wajen shawo kan kalubalen ita ce sulhu da zaman sasantawa da shiga tsakani da wanzar da adalci.

Abdulsalami, wanda Bishop din Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah ya wakilta, ya gargadi ’yan siyasa a kan sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa wata a cewarsa hakan na iya dagula kasar.

Ya ce:

“Wadannan sauya shekar suna haifar da rikici da kuma zafafa yanayin siyasar saboda son ran dan siyasa daya kawai. Sauya shekar da suke yawan yin na kara rura wutar rikice-rikice ne kawai.”

Ya kuma yi kira da a kara hadin kai tsakanin jami'an tsaro wajen tunkarar laifuka da sauran miyagun mutane.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Sannan ya sanya alamar tambaya game da sake tubabbun masu tayar da kayar baya tunanin da gwamnati ke yi, yana mai cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta fito fili ta bayyana wa mutane abubuwan da ake zargin ta da aikin sake wa tubabbun tunani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng