'Yan bindiga sun kashe mutum 19 a Katsina, sun ƙona gidaje sun sace dabbobi masu yawa

'Yan bindiga sun kashe mutum 19 a Katsina, sun ƙona gidaje sun sace dabbobi masu yawa

  • Yan bindiga sun kai hari kauyen Tsauwa a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina
  • Sun kashe mutane 19, wasu mutanen da dama ba a gansu ba kuma sun sace dabbobi tare da kona gidaje
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin tana mai cewa za a binciko wadanda suka kai harin a hukunta su

A kalla mutane 19 ne suka mutu sannan wasu dama an neme su an rasa bayan yan bindiga kan babura sun kai hari kauyen Tsauwa a karo na biyu a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina a yammacin ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani majiya daga kauyen ya ce maharan sun afka garin ne misalin karfe 5.45 na yamma.

Taswirar jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Yan bindigan sun tarwatsa mazauna kauyen suka rika binsu a kan babura, suka harbe 19 har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya kara da cewa maharan sun kuma kona gidaje da dama sannan sun sace shanu da wasu dabbobin.

Wani majiyan ya ce sun sanar da jami'an tsaro cewa an kawo musu hari amma ba a kawo musu dauki ba.

Majiya ta ce:

"Bayan barin kauyen, sun tafi kauyen Yar Lumo inda suka kwana suna shan kida, suna harba bindiga domin murnar nasarar da suka samu a Tsauwa."
"Mutum 19 sun mutu wasu da dama ba a gansu ba don haka babu tabbas ko za a same su da rai ko akasin haka."

Amma ya ce wani mazaunin garin da ke neman dan uwansa ya kira wayansa amma zai daya daga cikin yan bindigan ya amsa.

KU KARANTA: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Ya ce masa:

"Kun kashe biyu cikinmu, mu kuma mun ninka abin da kuka yi mana."

Sunayen wasu daga cikin wadanda suka mutu

Wasu daga cikin wadanda aka kashe sun hada da na'ibi Malam Bala (Rabe), Abdulmudallib, Sani Lawal (Atti), Suleiman Ashiru, Ashiru Lawal, Mannir Sanusi, Husamatu Kabir, Mansir Ayyau, da Shafiu Ayyau.

Saura sun hada da Alhaji Salisu, Abdulaziz Iliya, Umar Dan Shehu, Tukur Wada, Abubakar Mande, Malam Bawo, Abubakar Abdulmalik, Iliya Abdulmummuni, da Tukur Haruna duk mazauna kauyen kuma an musu jana'iza bisa koyarwa addinin musulunci.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce kwamishinan yan sanda Sanusi Buba ya ziyarci kauyen da kansa ya kuma bada umurnin a tabbatar an kamo wadanda suka kai harin su fuskanci shari'a.

'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

Rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.

A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.

Yayin da an kai gawar Sama'ila asibitin ƙwararru ta Rashid Shekoni da ke Dutse, Aliyu wanda ya tsira da harbin bindiga yana samun kulawa a asibitin na Shekoni da ke Dutse kamar yadda News Wire ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel