Abun bakin ciki: Masu garkuwa da mutane sun kashe jigon PDP da wata mata a Filato

Abun bakin ciki: Masu garkuwa da mutane sun kashe jigon PDP da wata mata a Filato

  • Wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun jefa karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato cikin firgici da bakin ciki
  • Hakan na faruwa ne yayinda aka kashe dan takarar kansila na jam'iyyar Peoples Democratic Party da wata mata a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni
  • Istifanus Gyang, sanata mai wakiltar Filato ta arewa ya tabbatar da kisan a wata sanarwa daga mai taimaka masa kan harkokin yada labarai

Mutanen unguwar Fobur, karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato sun shiga halin firgici biyo bayan kisan wani dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke neman kansila.

'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe jigon na PDP da wata mata a daren ranar Alhamis, 24 ga Yuni, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Karyane: Sojin Saman Najeriya Sun Karyata Jefa Bama-Bamai Kan Masu Daurin Aure

Abun bakin ciki: Masu garkuwa da mutane sun kashe jigon PDP da wata mata a Filato
Yan bindiga sun kashe jigon PDP da wata mata a Filato Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Istifanus Gyang ne ya tabbatar da kisan a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, a cikin wata sanarwa ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Ashoms.

Yayin da yake jajantawa dangin mamacin, Sanatan ya koka da yawaitar kashe-kashen da 'yan mazabar sa ke ci gaba da fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Tubabben dan IPOB ya jagoranci ‘yan sanda wajen kashe ‘yan ta’adda da lalata sansanoninsu a Imo

Ubah Ogaba, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar a yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana cewa yan sanda sun ceto mutum daya da aka yi garkuwa da shi.

Ogaba ya ce mafarauta guda biyu sun rasa rayukansu a kokarin ceto wanda aka sacen.

Matsalar Tsaro Yan Bindiga Sun Hallaka Matar Wani Tsohon Kwamishina

A wani labarin, wasu yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun kashe, Mrs. Olayemi Odetomi, matar tsohon kwamishinan ƙananan hukumomin jihar Oyo, Peter Odetomi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa matar mai kimanin shekara 66 a duniya an kashe ta ne a gidanta dake yankin Bodija-Ashi, Ibadan, jihar Oyo da safiyar ranar Jumu'a.

Mijin matar, Peter Odetomi, wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ogbomoso ne, ya riƙe muƙamin kwamishina a zamanin mulkin marigayi Abiola Ajimobi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng