Tubabben dan IPOB ya jagoranci ‘yan sanda wajen kashe ‘yan ta’adda da lalata sansanoninsu a Imo
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta kai wani mummunan hari a kan maboyar IPOB da ESN
- Jami'an bangarori daban-daban da tawagogin da babban sifeton 'yan sanda (IGP) ya kafa sun rusa sansanonin kungiyoyin a ranar Juma'a, 25 ga Yuni
- Jami'an tsaron wadanda tubabben tsohon dan ta'adda ya jagoranta sun kuma kawar da mambobin kungiyar
Mambobin kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) sun hadu da daidai su a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, lokacin da ‘yan sanda suka kai hari a sansanoninsu.
Wani babban jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sansanonin mallakar haramtattun kungiyoyin suna yankunan Izombie, Atta, da kuma Ideato North na Imo, jaridar The Sun ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun damke kasurgumin mai siyar da makamai ga ‘yan fashi a Katsina
Jami'in dan sandan ya bayyana cewa a yayin harin, an kashe mambobin kungiyoyin da dama a cikin dajin.
Ya kara da cewa, wani tubabben dan kungiyar IPOB wanda ya tona lamarin ga 'yan sanda shine ya jagoranci jami'an 'yan sanda na IGP Intelligence Response Team (IRT), STS, runduna ta musamman, AKU, QIT, da sauran rundunoni na musamman na jihar Imo zuwa maboyar kungiyoyin.
KU KARANTA KUMA: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Ɗaliban Kwalejin Fasaha 10 da Zargin Garkuwa da Abokin Karatunsu
Dan sandan ya ce:
“Dakarun sintiri na ‘yan sanda sun mamaye dukkan sansanonin bayan musayar wuta an kwato makamai da yawa, motocin sata, abubuwan fashewa, hodar bindiga, laya, tutocin IPOB / ESN, alburusai, wiwi, tramadol, da sauran miyagun kwayoyi da yawa."
'Yan sanda sun kame tsagerun IPOB 60 dake kai hare-hare da kone ofisoshin INEC
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta kama wasu mutane sama da 60 da ake zargi membobin kungiyar nan ce ta Biafra mai neman ballewa daga Najeriya.
Ana zargin mutanen cewa sune suka yi ta kai hare-hare kan ‘yan sanda da kona ofisoshin ‘yan sanda da kuma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar ta Ebonyi.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar yace an kwato bindigogi da albarusai da kunkuru mai rai da layu daga hannun wadanda ake zargin.
Asali: Legit.ng