Karyane: Sojin Saman Najeriya Sun Karyata Jefa Bama-Bamai Kan Masu Daurin Aure

Karyane: Sojin Saman Najeriya Sun Karyata Jefa Bama-Bamai Kan Masu Daurin Aure

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta karyata cewa ta jefa bama-bamai kan masu daurin aure
  • Rundunar ta ce rahoton ba komai bane face kokarin bata sunan rundunar da kuma ayyukanta
  • Hazalika ta bayyana yadda lamarin ya faru, tare da dagewa cewa 'yan bindiga suka ragargaza

Rundunar Sojin sama ta Najeriya ta bayyana rahotannin fashewar bam a wurin daurin aure a jihar Neja a matsayin wani yunkuri na bata sunan kokarinsu da sauran Hukumomin Tsaro, The Nation ta ruwaito.

Daraktan Hulda da Jama'a da Watsa Labarai na Sojan Sama na Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, a cikin wata sanarwa, ya musanta batun da cewa:

"Idan da gaske an kai hari kan masu daurin aure, tambayar da ya kamata 'yan Najeriya su yi ita ce 'Me ya sa za a daura aure a wani yankin dazuzzukan da ke da yawaitar ayyukan 'yan bindiga?

KU KARANTA: Bayan Shafe Shekaru 12 Yana Mulki, Firaministan Israi’la Ya Rasa Ikonsa

Ba Gaskiya Bane: Sojin Saman Najeriya Sun Karyata cewa sun jefa Bam masu daurin aure
Jirgin sama na yaki na Najeriya tare da jami'an sojin sama | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

“A bayyane yake cewa ayyukan hadin gwiwar NAF na baya-bayan nan, tare da Sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro, suna bayar da sakamakon da ake bukata kuma a bayyane yake, wasu mutane sun fito ne domin su bata wannan kokarin.

"Amma ku kwana da sanin cewa ba za mu mika wuya ga duk wani bata suna ba.

"NAF karkashin jagorancin shugaban hafsan sojojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, za ta ci gaba da kai hare-hare a wuraren wadannan masu aikata laifuka har sai mun fatattake su daga dukkan yankin kuma an dawo da zaman lafiya da tsaro gaba daya".

NAF ta yi ruwan bama-bamai kan masu daurin aure a jihar Neja

An ruwaito cewa jirgin NAF Alpha jet ya yi ruwan bama-bamai a wurin daurin aure a garin Genu da ke jihar Neja, inda ya kashe wasu bakin, PRNigeria ta ruwaito.

Harin wanda aka ce ya kashe wasu 'yan bindiga da barayin shanu ya faru ne a garin Genu da ke jihar Neja a ranar Asabar, ya kara da cewa "Daya daga cikin bama-baman da ake zargin ya kauce ne ya fada kan wani wajen daurin aure a wani kauye da ke kusa."

KU KARANTA: Manya Na Ku Daban: Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin, Sheikh Ahmad Gumi, wani malamin addinin Islama, kuma tsohon hafsan soji, a ranar Talata, ya bayyana cewa 'yan bindiga sun gaji kuma suna son a wanzar da zaman lafiya, PM News ta ruwaito.

Shehun malamin addinin musuluncin wanda ke zaune a Kaduna yayin tattaunawa da manema labarai ya ce 'yan bindigar a shirye suke su ajiye makamansu idan suka samu hadin kai na gaske daga gwamnati.

A cikin kalaman nasa: “Eh, gaskiya ne sosai saboda 'yan bindiga suna cewa yanayi ne ya ingiza su zuwa zama 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.