Da Dumi-Dumi: Bayan Shekaru 6, Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar EFCC

Da Dumi-Dumi: Bayan Shekaru 6, Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar EFCC

  • Shugaba Buhari ya nada sakatare ga hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC)
  • Hakazalika shugaba Buhari ya amince da nadin Mambobin Kwamitin hukumar ta EFCC bayan shekaru
  • Hukumar ta EFCC ta kasance ba tare da Mambobin Kwamiti ba na tsawon shekaru, tun shekarar 2015

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin George Abangeekpungu a matsayin sakataren hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC).

Nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ofishin babban lauyan Najeriya da ma'aikatar shari'a ta kasa, Umar Jibrila Gwandu ya sanyawa hannu a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewar sanarwar, wa'adin sabon nadin zai kasance na shekara biyar ne.

KU KARANTA: Hotunan yadda jama'ar Zaria suka yi wa 'yan bindiga sallar Al-Qunuti

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar EFCC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hakanan an nada Mambobin Kwamitin na EFCC da suka hada da Luqman Muhammad (Kudu maso Kudu), Anumba Adaeze (Kudu maso Gabas), Alhaji Kole Raheem Adesina (Arewa ta Tsakiya) da Alhaji Yahya Muhammad (Arewa maso Gabas).

Nadin ya yi daidai da Sashe na 2 (1) da Sashe na 4 na Dokar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa, 2004.

A cewar sanarwar, EFCC tana aiki ba tare da Membobin Hukuma ba tun shekarar 2015.

Tuni Shugaba Buhari ya ba da umarnin tura sunayensu don Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin.

Premium Times ta bayyana wani yankin sanarwar na cewa:

"Shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya ya nada George Abang Ekpungu a matsayin Sakataren Hukumar Yaki da Cin Hanci da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC)."

KU KARANTA: Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa

Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu

A wani labarin, Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce korafin tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, na hannun hukumar don ci gaba da bincike, Daily Trust ta ruwaito.

A wata hira ta musamman da jaridar ThisDay ta wallafa a ranar Lahadi, Bawa ya ce bincike ba ya karewa a cikin yini guda.

Ya ce:

“Kun yi min tambaya a baya game da kame mutane kafin bincike yanzu kuma kuna cewa me ya sa ba mu kama Tinubu ba? Me ya sa ba ku ce kawai 'a kame shi? ba'
“Ana ci gaba da bincike. Lokacin da kake bincika lamura irin haka, ba su karewa a rana guda.

Dubban bincike na ci gaba, a kowace rana. Bawa an ce ya nemi fom din bayyana kadarorin Tinubu lokacin da yake shugaban Ofishin shiyya na EFCC a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel