Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa
- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zaman tattaunawa da 'yan yankin kudu maso gabas
- Shugaban zai yi haka ne in ji rahoto don samar da zaman lafiya a yankin na kudu maso gabas
- A yanzu haka shugaban ya tura jami'ai da dama zuwa jihar Enugu a shirin tattaunawar dasu
Chris Ngige, Ministan kwadago, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karbar tattaunawa don magance rikicin dake faruwa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, The Nation ta rahoto.
A kwanakin baya kada, an yi ta kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati a duk fadin kudu maso gabashin kasar, lamarin da ya kai ga kashe jami'an tsaro da dama.
KU KARANTA: Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu
Yayin da ‘yan sanda da sojoji ke zargin kungiyar tsageru ta IPOB da kitsa hare-haren, kungiyar ta sha musanta cewa tana da hannu cikin barnar, The Cable ta ruwaito.
Har ila yau, an yi ta yin korafe-korafe da barna daga sassan kudu maso gabas na nuna bukatar ballewa daga Najeriya, yayin da masu ruwa da tsaki daban-daban su ma suka koka kan yadda aka mayar da yankin saniyar ware.
Sai dai, a cewar Ngige, gwamnatin tarayya na bin wasu hanyoyin don ganin cewa mutanen kudu maso gabas ba su "ji an ware su" a Najeriya ba.
Ministan yace:
"Mun kuma kalli yanayin tsaro, musamman a shiyya ta, kudu maso gabas, kuma mun gabatar masa da wasu shawarwari bisa dogaro da son mutane, da kuma abin da gwamnatin ma ke so.
“Muna bin diddigin tattaunawa, wanda a karshe, shi ne abin da zai faru. Dole ne muyi magana; dole ne mu tattauna. Wani bangare na tattaunawar zai fara gobe.
"Ministan tsaro, ministan cikin gida, da shugabannin hafsoshi sun kasance a Enugu ranar Asabar da ta gabata kuma za mu yi taro na gaba kan hakan.
KU KARANTA: Jami'an SSS Sun Sake Cafke Wani Mawaki da Ya Zagi Annabi a Jihar Kano
Gwamnatin Buhari ta zargi gwamnonin PDP da kin kawo karshen rikicin makiyaya
A wani labarin daban, Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ta zargi gwamnonin a karkashin jam’iyyar PDP, da kin goyon bayan kudirin kawo karshen rikicin makiyaya a kasar ta yadda za a ceci rayukan jama'a da dukiyoyinsu, BBC ta ruwaito.
Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan ne bayan taron da kungiyar Gwamnonin PDP ta gudanar a karshen mako a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a ranar Litinin.
A martaninta cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja, ya ce gwamnonin PDP ba su samar da mafita ga matsalolin kasar ba amma sun fi sha'awar abinda ya shafe su.
Asali: Legit.ng