Sace dalibai: Mun samu labarin shige da ficen ‘yan bindiga kafin harin makarantar Yauri – Gwamna Bagudu

Sace dalibai: Mun samu labarin shige da ficen ‘yan bindiga kafin harin makarantar Yauri – Gwamna Bagudu

  • Gwamna Atiku Bagudu ya bayyana cewa sun samu labarin shige da ficen 'yan bindiga a jihar Kebbi kafin harin Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yauri
  • Atiku ya ce a lokacin da suka samu wannan labari sai suka tuntubi makarantar don jin ta bakinsu, inda suka ce saura makonni biyu dalibai su kammala jarrabawa
  • Saboda daliban su samu damar yin jarrabawar sai aka tura jami'an tsaro, amma 'yan bindigan sun fi karfinsu domin sun zo ne a daruruwansu

Atiku Bagudu, gwamnan Kebbi, ya ce daga rahotannin da ya samu, ‘yan fashin da suka kai hari Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yauri, sun shigo a daruruwan su.

'Yan bindiga, a ranar Alhamis, sun mamaye makarantar sannan suka yi awon gaba da adadin dalibai da malamai da ba a tabbatar ba.

KU KARANTA KUMA: Za su dunga zuwa aiki sau 3 a sati tsawon wata 1 – Gwamnan Najeriya ya baiwa ma’aikata hutu

Sace dalibai: Mun samu labarin shige da ficen ‘yan bindiga amma sun sha kan jami’an tsaro – Gwamna Bagudu
Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu Hoto: The Cable
Asali: UGC

A wani samamen hadin gwiwa a safiyar ranar Juma'a, jami'an tsaron sun ceto wasu malamai da dalibai daga cikin wadanda aka sace, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yayin da yake jawabi ga iyayen daliban da aka sace a ranar Juma'a, Bagudu ya bayyana cewa jihar ta samu labarin shige da ficen 'yan fashi a kusa da makarantar makonni kafin harin, kuma ta tura karin jami'an tsaro.

Amma, ya lura cewa 'yan bindigar sun fi karfin jami'an, jaridar The Cable ta ruwaito.

“Tunda wannan mummunan lamarin ya faru, dukkan hannaye sr don tabbataur da ganin cewa an ceto wadannan yaran namu da ma’aikatanmu da ransu, cikin annashuwa da kuma jin dadi.
"Gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa ta hanyar dawo da wadannan yara da ma'aikatan lafiya," in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda wasu 'yan bindiga suka yi wa Malamin UNIBEN kisan gilla

“Tunda wannan mummunan lamarin ya faru, dukkan hannaye sun hadu don tabbataunr da ganin cewa an ceto wadannan yaran namu da ma’aikatanmu da ransu, cikin annashuwa da kuma jin dadi.
“Wannan satar ta kasance wani lamari mai ban tsoro da takaici, inda barayin suka yi arangama da‘ yan sanda wadanda ke tsaron makarantar. Abun takaici, sun tafi da wasu dalibai da malamai. Lamari ne mara dadi.
“Kimanin makonni biyu da suka wuce, akwai labarin shige da ficen ‘yan fashi kuma an gansu a kusa da wannan yankin. Mun tuntubi hukumomin tarayya a nan wadanda suka gaya mana cewa saura kimanin makonni biyu makarantar ta kammala jarabawarta. An amince cewa idan har za a sanya tsaro a makarantar, zai fi kyau a tallafa wa yaran su kammala jarabawarsu kafin su koma gida.”

Bagudu ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’an tsaro 22 daga runduna ta musamman mai yaki da ta’addanci, kafin harin.

“Sun kasance a wajen ko da aka kai harin jiya. Abin takaici, an fi karfin su, saboda baragurbin sun shigo a daruruwansu,” inji shi.
“Wadannan yaran duk namu ne kuma ya zama wajibi a kanmu mu yi addu’a don neman dawowar su lafiya. Na yi farin ciki cewa iyayen da suka yi magana sun nuna ƙarfin zuciya.
“Sun kuma yarda cewa jami'an tsaro sun yi iya kokarinsu kuma suna nan suna iya bakin kokarinsu, Haka kuma, hukumomin makarantar, shugaban makaranta, malamai da sauran ma'aikata. Da yardar Allah, yaranmu za su dawo gare mu."

Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC Sama da 80

A gefe guda, wasu rahotanni daga jihar Kebbi sun bayyana cewa jami'an rundunar soji sun yi gumurzu da yan bindigan da suka sace dalibai a makarantar gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri, jihar Kebbi, inda suka hallaka aƙalla 80.

Wasu shaidu sun tabbatar wa BBC cewa sun ƙirga aƙalla gawar masu garkuwan guda 80, waɗanda sojoji suka hallaka.

Shaidun sun ƙara da cewa an yi musayar wuta sosai tsakanin jami'an rundunar soji da kuma yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel