Hawaye sun kwaranya yayinda wasu 'yan bindiga suka yi wa Malamin UNIBEN kisan gilla

Hawaye sun kwaranya yayinda wasu 'yan bindiga suka yi wa Malamin UNIBEN kisan gilla

  • Matsalar rashin tsaro a kasar na ci gaba da zama abin tsoro ga dukkan 'yan Najeriya na gida da waje
  • Wani malamin UNIBEN, Maxwell Eseosa Aimuen, ya gamu da ajalin sa a hannun wasu ‘yan bindiga a ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, a garin Benin
  • Jami'in hulda da jama'a na makarantar, Benedicta Ehanire ya tabbatar da afkuwar lamarin, a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe Maxwell Eseosa Aimuen, malami a jami’ar Benin (UNIBEN) a garin Benin, babban birnin jihar Edo.

Jaridar PM News ta bada rahoton cewa hukumomin makarantar a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, sun tabbatar da kisan Aimuen.

KU KARANTA KUMA: Sace daliban Kebbi: Mun gazawa yaranmu, Shehu Sani ya koka

Hawaye sun kwaranya yayinda wasu 'yan bindiga suka yi wa Malamin UNIBEN kisan gilla
Hukumomin makarantar a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, sun tabbatar da kisan Maxwell Eseosa Aimuen Hoto: University of Benin.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Aimuen ya fara aiki a makarantar a shekarar 2015 a sashin karatun kula da harkokin gwamnati a matsayin mataimakin lakcara kuma ya kasance lakcara na II har zuwa rasuwarsa.

Benedicta Ehanire, mai magana da yawun jami’ar, ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun kashe malamin mai shekaru 33 ne a ranar Asabar, 12 ga Yuni, yayin da yake shiga cikin gidansa a Isihor, ‘yan sa’o’i kadan bayan ya rabu da abokansa a Ugbowo yankin birnin.

KU KARANTA KUMA: Masu magana da yawun Buhari su ne babbar matsalarsa - Gwamnonin PDP

A cewar rahoton, ‘yan bindigar sun harbi marigayin sau da dama kafin suka tsere daga wurin, ba tare da cire komai daga motarsa ba.

An tattaro cewa nan take aka kai rahoton lamarin ga yan sandan yankin Ugbowo da ke cikin garin.

Mutuwar Aimuen babban rashi ne ga UNIBEN

An tattaro cewa Endurance Aigbe, abokin aikin malamin da aka kashe, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Aigbe ya ce:

"Na kasance tare da marigayin har zuwa 8:00 na dare tare da wasu abokai inda dukkanmu muka tafi gidajenmu mabanbanta."

Daily Trust ta kuma ruwaito cewa kakakin UNIBEN din, wanda ya bayyana marigayin a matsayin ma’aikaci mai kwazo da himma, ya yi kira ga jami’an tsaro da su bankado wadanda ke da hannu a kisan.

Ɗalibar makarantar Kebbi ta yi ƙarin haske kan ƴan bindiga

A wani labarin, wata daliban makarantar FGC Birnin-Yauri a jihar Kebbi wacce ta tsira daga harin a ranar Alhamis ta ce bata tunanin yan bindigan da suka kai hari makarantansu yan Nigeria ne, The Cable ta ruwaito.

A ranar, Alhamis ne yan bindiga suka kutsa makarantar a kan babura suka kuma yi awon gaba da malamai da dalibai da dama.

Yayin harin, yan sanda da ke makarantar sun yi kokarin dakile harin amma yan bindigan sun fi su yawa hakan ya yi sanadin rasuwar jami'in dan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel