Za su dunga zuwa aiki sau 3 a sati tsawon wata 1 – Gwamnan Najeriya ya baiwa ma’aikata hutu
- An ba wa ma'aikatan gwamnati da ba su da muhimmanci a jihar Benuwe damar zuwa gonakinsu na ranakun Alhamis da Juma'a
- Gwamnatin jihar ce ta bayar da wannan umarnin a ranar Juma’a, 18 ga watan Yuni, ta ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati
- Gwamnatin Benuwai ya lura cewa ranakun hutun ana nufin taimakawa ne don bunkasa bangaren noma musamman a lokacin noman
Gwamnatin Benuwai ta bayyana cewa an bayar da hutun ne da nufin bunkasa harkar noma musamman a wannan lokaci na damuna
Gwamnatin jihar Benuwe ta bakin shugabar ma’aikatan gwamnati, Veronica Onyeke, ta bayyana ranakun Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutu ga ma’aikatan gwamnati domin su je gonakin su.
KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi yayin da 'yan gudun hijira a Taraba suka koma gidaje da gonakinsu
A bisa ga umarnin gwamnatin, an yanke shawarar ne don ba noma karfi domin bunkasa harkar noma a jihar.
Gwamnatin ta bayyana a fili cewa hutun da zai kare a watan Yuli, ba na muhimman ma'aikata bane a jihar, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda wasu 'yan bindiga suka yi wa Malamin UNIBEN kisan gilla
Wani bangare na umarnin ya ce:
“Dangane da haka, daga ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni zuwa 30 ga watan Yuli, 2021, an kaddamar da Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutun aiki.
“Don haka an shawarci ma'aikatan gwamnati da su yi amfani da wadannan ranakun wajen yin aikin noma da sauran abubuwan da suka shafi aikin gona.”
Makiyaya sun kashe manoma 100 a garuruwan Benuwe hudu
A wani labarin, mun ji a baya cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kashe sama da mutane 100 a karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benuwe.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa kisan ya fara ne a daren Juma’a, 21 ga Mayu, har zuwa safiyar Litinin, 24 ga Mayu.
Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Alfred Atera, ya tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukansu daga lamarin.
Asali: Legit.ng