Dalilai 4 da suka sa Buhari ya samu ƙasaitaciyyar tarba a Borno

Dalilai 4 da suka sa Buhari ya samu ƙasaitaciyyar tarba a Borno

  • Mutanen jihar Borno sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari tarba da arziki a ziyarar da ya kai a baya-bayan nan
  • Akasin yadda wasu suka yi masa ihu a ziyarar da ya kai a Fabrairun 2020, wannan karon jinjina da maraba aka yi masa
  • Akwai wasu dalilai da suka saka mutanen Borno suka sauya zukatan su game da Shugba Buhari

Shugaba Muhammmadu Buhari, a ranar Alhamis 17 ga watan Yuni ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar da na tarayya suka yi.

Shugaban kasar kuma ya yi amfani da wannan damar domin ganawa da dakarun sojojin Nigeria da ke fafatawa da yan Boko Haram a jihar ta arewa maso gabashin Nigeria.

Shugaba Muhammadu Buhari a yayin da kai ziyara Maiduguri, jihar Borno
Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da ke yi wa sojoji jawabi yayin ziyarar da ya kai jihar Borno. Hoto: Audu Marte/AFP
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Bana tunanin ƴan Nigeria ne: Ɗaliban makarantar Kebbi ta yi ƙarin haske kan ƴan bindiga

Ba kamar ziyarar da ya kai a Fabarairun 2020 inda wasu mazauna jihar suka yi masa ihu ba, wannan karon an masa tarbar ban girma inda mutane suka yi layi a gefen titi suna ta masa jinjina.

Legit.ng ta lissafo dalilai hudu da suka sa wannan karon ba a yi wa shugaban kasar ihu ba.

1. Yaki da Boko Haram ya dauki sabon salo

A cikin watannin da suka gabata, sojojin Nigeria sun kara zage damtse da karsashi a yakin da suke da yan ta'adda a Borno. Hakan yasa mazauna jihar sun fara samun natsuwa a zukatansu musamman bayan sauyin manyan hafsoshin sojoji da shugaban kasar ya yi.

2. Amsa bukatun Gwamna Zulum cikin gaggaawa

A lokacin da yan ta'adda suka yawaita kaiwa sojoji hare-hare, gwamnan Borno Babagana Zulum ya kan garzaya fadar shugaban kasa a Abuja domin neman dauki. Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce a koyaushe shugaban kasar amsa bukatun gwamnan hakan na saukaka yaki da yan ta'addan. Shi kuma Zulum a bangarensa ya kan koma gida ya shaidawa mutanen jiharsa irin taimakon da ya ke samu daga shugaban kasa.

3. Jagoranci na gari da Zulum ke yi a matsayin gwamnan Borno

Gwamna Zulum ya yi fice cikin gwamnoni saboda iya mulki da tafiyar da harkokin gwamnati tare da shayar da mutanensa romon demokradiyya hakan yasa mutane suna kaunar shugaban kasar duba da cewa dukkansu yan jam'iyyar APC ne.

KU KARANTA: 'Yan daba sun kutsa cikin kotu sun fatattaki alƙali saboda rikicin sarauta

4. Tsarin samar da gidaje da gwamnatin tarayya ta kadamar a jihar Borno

Yayin ziyararsa, Shugaban kasa ya kaddamar da gidaje 4,000 da ke cikin tsarin samar da gidaje na gwamnatinsa. Shugaban kasar ya kaddamar da gidaje 10,000 na farko wadanda ya amince kuma ya bada kudade a gina su domin mutanen da suke sansanin yan gudun hijira su samu sabbin matsugunai. Wannan tsarin samar da gidajen shine mafi girma da gwamnatin tarayya ta yi a jiha guda. Hakan na iya jefa kaunar shugaban kasar a zukatan yan Borno.

A wani labarin da Legit.ng ya kawo kun ji cewa Muhammadu Buhari ya gagara boye farin cikinsa a ranar Alhamis a Maiduguri bayan da ya kaddamar da ayyuka bakwai cikin 556 da Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya aiwatar cikin shekara biyu da ya yi a kan karagar mulki.

Gwamna Zulum da kansa ya bayyana haka a jawabin da ya saki ranar Alhamis a shafinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel